LABARAI/NEWS

Ƙin Sakin Nnamdi Kanu da Buhari yayi, Najeriya zata wargaje– lauyar Nnamdi.

Ƙin Sakin Nnamdi Kanu da Buhari yayi, Najeriya zata wargaje– lauyar Nnamdi.

Babban Lauyan Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biafra, IPOB, Nnamdi Kanu, Mike Ozekhome, ya yi gargadin ci gaba da tsare masu fafutukar kafa ƙasar ta Biafra.

Ozekhome ya ce Najeriya za ta wargaje idan ba a saki Kanu daga tsare ba nan ba da jimawa ba duk da kotu Ya yi wannan gargadin ne a wata ganawa da shugabannin kabilar Igbo a birnin Atlanta na ƙasar Amurka.

 

 

Ozekhome ya bada tabbacin cewa sakin Kanu ba zai haifar da rashin tsaro a yankin kudu maso gabas ba.

A cewar Ozekhome: “Muna nan a Kotun Koli, kuma za ta gyara kuskuren domin babu wanda zai tsorata kotun koli. Za su yi wani abu don kada Nijeriya ta wargaje.

“Na shaida wa kotu cewa sakin Kanu ba zai fasa Kudu maso Gabas ba ko kuma ya kawo tashin hankali a shiyyar. A maimakon haka, abin da zai kwantar da hankalin Kudu maso Gabas kenan.

Gwamnatin Najeriya ta ki sakin mai tada hankali duk da hukuncin da wata kotu ta yanke na cewa a sake shi Tun a watan Yunin 2021 ake tsare da Kanu, a lokacin da aka kama shi a Kenya aka mayar da shi Najeriya.

A ƴan watannin da suka gabata ne kotun daukaka ƙara da ke Abuja ta umarci gwamnatin Najeriya da ta saki Kanu Sai dai gwamnatin Najeriyar ta daukaka kara kan hukuncin kotun.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button