Ƙungiyar Marubutan Arewa Arewa Media Writers Tana Kira Ga Gwamnatin Jihar Gombe Da Ta Kuɓutar Mana Da Ɗan Uwan Mu Daga Hannun Yarbawa A Jihar Anambra

Ƙungiyar Marubutan Arewa Arewa Media Writers Tana Kira Ga Gwamnatin Jihar Gombe Da Ta Kuɓutar Mana Da Ɗan Uwan Mu Daga Hannun Yarbawa A Jihar Anambra
Ƙungiyar marubutan Arewa Arewa Media Writers ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, tana kira ga Gwamnatin jihar Gombe, da sarakuna, Malamai, da masu hannu da shuni dasu taimaka wajen kuɓutar mana ɗan uwan mu Ibrahim Abubakar daga hannun hukumar ƴan sanda ta jihar Anambra.
Ibrahim Abubakar matashi ne, ɗan garin Hashidu a ƙaramar hukumar Dukku dake jihar Gombe, wanda hukumar ƴan sanda ta jihar Anambra ta cafke shi a lokacin da yake achaɓa a jihar, hakan ya faru ne a lokacin daya ɗauki wani bafulatani daga iyakar jihar Enugu zuwa Okka dake ƙaramar hukumar Garke a jihar Anambra.
Hakan ya faru ne a dai-dai checking point, na jami’an tsaro, inda suka tsaya domin binciken kayan su, tsayawar su keda wuya kenan sai bafulatani ya gudu ya bar dan acaɓan da kayan sa.
A cikin binciken da jamian tsaron sukayi, sun gano cewa, akwai bindiga cikin kayan bafulatanin daya gudu, hakan ya sa hukumar ƴan sanda suka miƙa shi zuwa chaji office, tare da yi masa tambayoyi, sai dai Ibrahim Abubakar ya bayyana cewa, bai san komai ba, hasali ma a hanya ya tare shi, amma hakan bai sa hukumar ƴan sanda sun amince da maganar sa ba.