ylliX - Online Advertising Network Ƴan Banga Sun ragargaza yan Bindiga Sun kashe wasu daga cikin su A Katsina - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ƴan Banga Sun ragargaza yan Bindiga Sun kashe wasu daga cikin su A Katsina

Ƴan Banga Sun ragargaza yan Bindiga Sun kashe wasu daga cikin su A Katsina Ƴan banga sun yi nasarar fille kan wani gawurtaccen dan bindiga tare da kama wasu shida da ransu a Jihar Katsina

Yan bindigar sun kwashi kashinsu a hannun yan bangar ne a wani harin bata garin da yan banga suka dakile a Karamar Hukumar Batsari ta jihar
Alkaluman da muka samu na yan bindigar da aka kashe sun sha bamban amma majiyoyinmu sun tabbatar cewa an kama yan bindiga akalla shida

Wasu majiyoyi a Batsari sun ce yan bindiga tara aka kashe wasu kuma na cewa daya shida ne a yayin da wasu suka ce mutum daya ne
Amma wani bidiyo da ka yada bayan artabu ya nuna wata gawa da aka file wa kai tare da sare kafarta daya

Akwai wani bidiyo kuma da ya nuna mutanen garin suna murna kan nasarar da yan bangar suka samu tare da nuna kai da kafar dan bindigar da aka kashe Wata majiya a Karamar Hukumar Batsari ta shaida wa wakilinmu cewa yan bindigar sun kai hari garin ne da yamma ranar Lahadi suna harbi inda suka kashe mutum daya suka kuma sami wani da harbi

Bayan nan ne rundunar hadin gwiwar yan banga da Civilian JTF da jami’an tsaro suka kawo dauki suka kashe daya daga cikinsu tare da tsare wasu da dama Wata majiyar ta ce yan bindigar da aka kashe sun kai mutum tara an kuma tsare wasu biyar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button