ylliX - Online Advertising Network Ƴan bindiga sun kai hari garin bakori da Dukke ta Funtua inda suka sace mutane tare da kashe mutum hudu - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ƴan bindiga sun kai hari garin bakori da Dukke ta Funtua inda suka sace mutane tare da kashe mutum hudu

Ƴan bindiga sun kai hari garin bakori da Dukke ta Funtua da Ciɓauna ta Dandume inda suka sace mutane tare da kashe mutum hudu

Yan bindiga sun shiga cikin garin Dukke dake daf da shiga cikin garin Funtua kan hanyar Funtua zuwa Gusau, inda majiyar ta bayyana mana cewa bayan yan bindigar sun fara harbe-harbe wajen 11:30pm na daren jiya Jumu’a sun yi nasarar yin garkuwa da wani dan kasuwa a garin Alh Murtala Fari, da kuma matar kansilan garin

Haka kuma duk a kusan lokacin ƴan bindigar sun shiga Unguwar Ciɓauna inda bayan sun yi ta harbe-harbe sun kashe mutum 4 tare da yin awon gaba da dukiya

Sai dai kawo haɗa wannan rahoton Katsina Media Post News ba ta sami wani rahoton faruwar lamarin daga ɓangaren yan sanda ba

A iya cewa a yan kwanakin nan, bayan samun sauƙin kai hare-hare a baya, yanzun abin na kokarin dawowa sabo, na kai hare-hare nan da can, inda har cikin birnin Katsina a yan kwanakin nan maharan sun shige ta sau biyu suka dauki mutane

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button