ylliX - Online Advertising Network Ƴan bindiga sun kashe mutane a masallaci juma'a a jihar Zamfara - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ƴan bindiga sun kashe mutane a masallaci juma’a a jihar Zamfara

Ƴan bindiga sun kashe mutane a masallaci juma’a a jihar Zamfara

Sun kashe mutum ne suka mutu wasu kuma da dama suka jikkata a wani harin da a ka kai a wani masallaci a jihar Zamfara

Kamfanin Dillacin Labarai na Reuters ya ruwaito cewa lamarin ya faru ne a Ruwan Jema da ke yankin karamar hukumar Bukkuyum a jihar, inda ‘yan bindigar a kan babura suka nufi masallacin a yammacin ranar Juma’a suka fara harbi kan-mai-uwa da wabi

Harin na zuwa ne makonni uku bayan da aka sace wasu masallata a masallacin Zugu na karamar hukumar

A watan Yuli ma ‘yan bindigar sun kai hari a yankin tare da sace mutane da dama domin karbar kudin fansa
Ana tsammanin dai ƴan bindigar na da sansani kusa da kauyen, abin da ya sa suke matsa ma wa yankin da hare-hare kenan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button