Latest Hausa Novels

Ƴan binidga sun kashe sojoji 85 yan sanda 65

Ƴan binidga sun kashe sojoji 85 yan sanda 65
Yayin da matsalar tsaro ke ƙara muni rahotanni sun nuna cewa an kashe ‘yan sanda 65, sojoji 85 tsakanin Janairu zuwa Yuni, 2022

Baya ga wannan adadin rahotannin sun kuma tabbatar an kashe sauran ba’arin jami’an tsaro waɗanda ba sosoji da yan sanda ba har su 92
Waɗannan adadi ne dai da kafafen yaɗa labarai su ka buga. An tabbatar akwai da dama waɗanda ba a lissafa ba, saboda ba su cikin rahotannin kafafen yaɗa labara

ya fayyace yawan jami’an tsaron da aka kashe a Kudu maso Gabas Kudu maso Yamma Kudu maso Kudu da Arewa ta Tsakiya Ya kuma ƙididdige yawan waɗanda aka kashe a Arewa maso Yamma Arewa maso Gabas

Yayin da Arewa maso Gabas ke fama da Boko Haram Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya na fama da ‘yan bindiga, Kudu maso Gabas kuma na fama da ‘yan ESN, mayaƙan IPOB masu rajin sai sun kafa ƙasar Biafra sun nuna an bindige jami’an tsaro 157 yayin da kuma aka kashe farar hula kimanin 3000 a watannin

Aƙalla an kashe mutum 35,000 a rikicin Boko Haram daga 2009 zuwa 2022, yayin da sama da mutum miliyan uku su ka rasa muhallin su A kan matsalar tsaro cikin makon jiya ne ‘yan ta’adda su ka kai wa dogaran tsaron Buhari hari, su ka kashe sojoji takwas Mahara sun kai wa Dakarun sojojin Bataliya ta 7 ta Dogaran Shugaban Ƙasa hari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button