LABARAI/NEWS

Ƴan Boko Haram Sama Da 70 Sun Nitse A Ruwa Bayan Harin Sojoji Ta Sama A Borno

Ƴan Boko Haram Sama Da 70 Sun Nitse A Ruwa Bayan Harin Sojoji Ta Sama A Borno

’Yan ta’addan Boko Haram sama da 70 sun nitse a wani kogi bayan wani harin da dakarun rundunar tsaro ta Operation Hadin Kai suka kai musu ta sama a jihar Borno

Rahotanni sun nuna ko gabanin wannan farmakin ma, sojojin sun kai wani hari tare da hadin gwiwar rundunar tsaron fararen hula ta CJTF, inda suka kashe ’yan Boko Haram sama da 20 a kauyen Shehuri da ke karamar hukumar Bama a jihar ta Borno ranar Alhamis

Majiyoyi daga yankin sun ce bayan harin na Shehuri yan ta’addan da ke kokarin tserewa sun nitse a wani kogi da ke kusa da kauyen Dipchari a karamar hukumar Bama, ranar Juma’a

Yan ta’addan sun kwashi kashinsu a hannu; sun rasa sama da mayaka 70 a kusa da kauyen Dipchar Yanzu haka ma ana kan gano wasu gawarwakin nasu inji wata majiya daga jami’an tsaro

Ita ma wata majiya da take yankin, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta ce bayan faruwar lamarin, an ga ’yan ta’addan na ta kokarin tsamo gawarwakin ’yan uwan nasu daga kogin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button