LABARAI/NEWS

Ƴan Iskan gari a Kano ɗauke da Muggan Makamai Sun aukawa Mabiya Shi’a

Ƴan Iskan gari a Kano ɗauke da Muggan Makamai Sun aukawa Mabiya Shi’a

Ƴan iskan gari wanda muka Samu tabbacin cewa Aksarin su Matasa ne sun aukawa mabiya Shi’a a garin Kano Kwanar Dala a jiya Suna tsaka da gudanar da gwanon Maulidin Nana Faɗima (AS)

 

Mabiya Shi’ar bayan sun hau sahu suna tafe suna rera waƙen yabo ga ɗiyar Manzon Allah (SAW) nana Faɗima (AS) domin tunawa ranar Haihuwarta

 

 

ba zato bare tsammani a dai-dai kwanar Dala ga wasu Matasa ɗauke da duwatsu wasu da maggan Makamai suka shiga jifan mabiya Mazhabin Shi’ar mata da maza yara da manya tare da Sara Suka kan mai uwa da wabi

 

Sanadiyar wannan aukawar da waɗannan ƴan iskan gari sukayi akan Mabiya Shi’a yayi Sanadiyar samun raunuka na wasu daga cikin ƴaƴan Mazhabin Shi’ar Bugu da ƙari ba’a rasa rai ko da na Mutum ɗaya ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button