LABARAI/NEWS

ƳAN NAJERIYA Rashawa ce ta fitar da ni daga ofis in ji Magu

ƳAN NAJERIYA Rashawa ce ta fitar da ni daga ofis in ji Magu

Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta’annati EFCC Ibrahim Magu ya ce babu hujjar fitar shi daga hukumar EFCC.

Magu ya bayyana hakan ne a yayin wani bikin bayar da lambar yabo da kungiyar daliban matan arewa ta shirya domin girmama shi a ranar Lahadi a Abuja.

Ni ina daga cikin mutanen da rashawa ta yaka, amma ina farin ciki kan abubuwan da suke faruwa a yanzu gaskiya na bayyana ga ‘yan Najeriya in ji shi

Magu wanda dansa Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu ya wakilta, ya yabawa kungiyar game da girmama shi da ta yi da wannan lambar yabo ta cancanta kuma yace yana cike da murnar karbar kyautar

Da take nata bayanin kakakin kungiyar Aisha Nasir ta bayyana magu a matsayin wani mutum na daban, kuma jajurtacce, abin da ya sa ya cancanci kyautar kenan

Ko kana so ko baka so Ibrahim Magu ya kai EFCC wani mataki a Najeriya wanda mutane da dama ba su taba zaton za ta iya kai wa ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button