LABARAI/NEWS

Ƴan samogal sun kashe jami’in kwastam 1 da jikkata 3

Ƴan samogal sun kashe jami’in kwastam 1 da jikkata 3

Wasu da ake zargin ƴan samogal ne sun kashe wani jami’in hukumar kwastam ta ƙasa a ranar Juma’a mai suna Igboho a lokacin da yake sintiri a hanyar Sinau-Kenu a Ƙaramar Hukumar Baruteen a jihar Kwara.

Kakakin hukumar kwastam na jihar Kwara, Chado Zakari ne ya bayyana haka a garin Ilorin a jiya Litinin, inda ya ce tun da fari rundunar ƴan sandan ta kama buhu 40 na shinkafar da aka yi smogal ɗin ta da jarkokin man fetur 30 da aka ɓoye a wani daji da ke kusa da titin Sinau-Kenu.

Wadanda ake zargin ‘yan smogal ne su ka yi kwanton-bauna tare da harbe-harbe a kan motar sintiri da ke jigilar kayayyakin da aka yi fasa-kwaurin zuwa ma’ajiyar gwamnati.

A musayar wutar da ta barke, jami’i guda ya mutu, yayin da jami’ai uku suka samu muggan raunuka kuma a halin yanzu suna kwance a asibiti.

Marigayin, mataimakin Sufeto, Saheed Aweda, an binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a mahaifarsa, Popogbona a karamar hukumar Ilorin ta yamma a jihar Kwara.

Zakari ya ce Kwanturolan kwastam, Olugboyega Peters, ya ziyarci iyalan mamacin don jajanta wa.”

Ya kara da cewa Peters ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan harin domin gano masu laifin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button