LABARAI/NEWS
Ƴan Sanda a jihar Neja ta yi Nasarar cafke Wasu masu Garkuwa da mutane

Ƴan Sanda a jihar Neja ta yi Nasarar cafke Wasu masu Garkuwa da mutane
Rundunar ‘yan sandan ta cafke wasu Mutane biyu da Ake tuhuma da laifin Garkuwa da Mutane
Kakakin rundunar ya bayyana cewar wadanda Ake tuhumar sun ce su na cikin wadanda ke addabar yankunan Kaffin Koro da ke Karamar Hukumar Paikoro da kuma Gwagwalda ta yankin Babban birnin Tarayya Abuja
Rundunar kuma ta ku6utar da mutane Bakwai cikin wadanda a ka yi Garkuwar da su tare da samun tsabar kudi Naira Miliyan uku da kuma wayar salula guda uku
Da kuma mugaye makamai a hanun su inda a yanzu Wanda ake zargi da garkuwa da mutane suna hanun hukma domin ai masu hukunci abin da suka aikata