LABARAI/NEWS

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe

Rundunar yan sandan jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta ja hankalin yan siyasa bisa yaƙin neman zaɓe mai tsafta
Jan hankalin rundunar ya zo ne a dai dai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta buɗe damar yaƙin neman zaɓe a hukumance

Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano Abubakar Lawan, ya gana da yan takarar jam’iyyu daban-daban domin ganin yadda za a yi yaƙin neman zaɓe, cikin kwanciyar hankali ba tare da samu tashin hankali ba.

Da yakewa ƴan jarida ƙarin haske kan abinda taron ya kunsa kakakin rudunar yan sandan jihar Kano Sifiritandan yan sanda Abdullahi Haruna Kiyawa, ya yace sun tattauna batutuwa da dama da suka shafi yakin neman zaɓe na shekarar 2023 da hukumar zaɓe ta buɗe a ranar 28 ga watan Satumba na wannan shekara da muke ciki

Kwamishinan ƴan sandan ya umarci ƴan takarar da kowa, ya kawo jadawalin kamfe ɗin sa domin tabbatar da bawa kowa tsaro yadda ya kamata ya ƙara jan hankalin su a kan cewa su jawa magoya bayan su kunne, kada a samu matsala wani ya ce zai abinda ba shi bane inji Kiyawa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button