ylliX - Online Advertising Network Ƴan ta'adda da dama sun baƙunci lahira bayan da Sojojin Saman Najeriya suka yi luguden wuta a maɓuyar su a Kaduna - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ƴan ta’adda da dama sun baƙunci lahira bayan da Sojojin Saman Najeriya suka yi luguden wuta a maɓuyar su a Kaduna

Ƴan ta’adda da dama sun baƙunci lahira bayan da Sojojin Saman Najeriya suka yi luguden wuta a maɓuyar su a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta samu bayanai daga rundunar sojojin saman Najeriya da ke aikin sintiri ta sama a kan wasu gungun ‘yan bindiga da aka gano a fadin jihar.

 

 

An samu nasarar kashe ‘yan bindiga da dama, tare da lalata sansanonin ‘yan bindiga daban-daban, yayin da wasu da aka yi garkuwa da su suka samu kuɓuta.

Samuel Aruwan, Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, ya ce a yankin Kawara da ke ƙaramar Hukumar Igabi, an kashe ‘yan bindiga uku, yayin da aka sako wasu da aka yi garkuwa da su kamar yadda jaridar Arewa Trends ta ruwaito.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button