LABARAI/NEWS

Ɗalibar firamaren da ake kyautata zaton ta fi tsufa a duniya, Priscila Sitienei, ta rasu

Ɗalibar firamaren da ake kyautata zaton ta fi tsufa a duniya, Priscila Sitienei, ta rasu

Marigayiyar wadda aka fi sani da sunan Gogo (wato kaka a harshen Kalenjin) ta rasu ne tana da shekara 99 a ranar Laraba a kasar Kenya.

BBC Hausa ta ruwaito cewa, dattijuwar ɗaliba ce a makarantar Vision Preparatory School da ke garin Ndalat kuma ta shirya rubuta jarabawar kammala firamare shekara mai zuwa, inda za ta cika shekara 100.

 

 

Jikanta mai suna, Sammy Chepsiror, ya shaida wa BBC cewa Gogo ta fara rashin lafiya ne tun a ranar Larabar da ta gabata bayan ta dawo daga makaranta – inda ta ce masa kirjinta na ciwo.

Shekaru da dama da suka wuce, marigayiyar tana aiki ne a matsayin ungozoma a ƙauyen su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button