ylliX - Online Advertising Network Ɗalibar Makarantar FGC Yawuri Ta Haihu A Wajen Masu Garkuwa Da Mutane - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Ɗalibar Makarantar FGC Yawuri Ta Haihu A Wajen Masu Garkuwa Da Mutane

Ɗalibar Makarantar FGC Yawuri Ta Haihu A Wajen Masu Garkuwa Da Mutane

 

Daya daga cikin ’yan makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) Birnin Yauri da ke jihar Kebbi, wacce ’yan bindiga suka sace a 2021 ta haihu a hannun masu garkuwa da ita.

Kafar yada labarai ta PRNigeria ta rawaito cewa dalibar mai shekara 16 na daya daga cikin ’yan mata 11 da har yanzu ba a sako ba tun bayan sace sama da su 100 da malamansu takwas, ranar 17 ga watan Yunin 2021.

 

 

Wata majiya mai tushe ta tabbatar wa kafar cewa dalibar, wacce har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a kai ga tantance sunanta ba, ta haifi da namiji ne a sansanin ’yan bindigar.

Majiyar ta shaida wa kafar cewa iyayen yaran na cike da damuwa kasancewar har yanzu an ki sakin ’ya’yan nasu, duk kuwa da biyan kudin fansa da musayar fursunonin da aka yi da ’yan ta’addan.
Majiyar ta ce, “Lokacin da gwamnati, musamman Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ta ce sam ba za ta tattauna da ’yan bindigar ba da ke bukatar biyan fansa ba, sai iyalan yaran suka tattara taro da kwabo don karbo yaran nasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button