LABARAI/NEWS

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

Ɗan China da ake zargi da kisan Ummita ya ce Naira Miliyan 60 ya kashe mata

A yau Laraba ne dai ɗan Chinan nan mai suna Frank Geng Quangrong wanda ake zargi da kisan masoyiyar sa Ummukulsum Sani wacce aka fi sani da Ummita ya fara kare kansa a kotu

 

Quangrong ya shaida wa kotun cewa shi Musulmi ne kuma ya na aiki a wani kamfanin tufafi a kasuwar Kantin Kwari ta jihar Kano

 

 

Ya bayyana cewa sun haɗu da marigayi Ummita ne a 2020 bayan da ta samu lambar wayar sa a wajen wata kawar ta
inda ta nuna tana son shi kuma za ta aure shi

 

ɗan Chinan ya ce bayan ya amince da ita sai su ka fara soyayya inda ta riƙa karɓar kuɗaɗe a wajen sa ya ƙara da cewa haka na riƙa bata duk abinda ta roke ni sabo da bana son na ɓata mata rai Na kashe mata kimanin Naira miliyan 60

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button