LABARAI/NEWS

Ɗan shugaban kasar Guinea ya sace jirgin sama mallakar gwamnati kasar

Ɗan shugaban kasar Guinea ya sace jirgin sama mallakar gwamnati kasar

An kama daya daga cikin ƴaƴan shugabaan Equatorial Guinea kan zargin sa da sace tare da sayar da wani jirgin sama mallakin gwamnatin kasar

 

an tsare Ruslan Obiang Nsue a ranar Litinin sannan aka yi masa daurin talala kamar yadda kafar talabijin ta kasar ta bayyana

 

Tun a cikin watan Nuwamban da ya gabata aka kaddamar da bincike bayan hukumomi sun gano cewa daya daga cikin jiragen gwamnati ya yi batan-dabo a filin jiragen sama na kasa da kasa

 

A shekarar 2018 ne aka tura wannan jirgin zuwa kasar Spain domin kula da lafiyarsa yayin da aka zargi Obiang da sayar da shi ga wani kamfanin mai kula da lafiyar jirage

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button