𝐋𝐀𝐑𝐔𝐑𝐀𝐑 𝐓𝐒𝐀𝐑𝐆𝐈𝐘𝐀 – 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐅𝐈𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈 𝐃𝐀 𝐉𝐈𝐍𝐈 [𝐁𝐈𝐋𝐇𝐀𝐙𝐈𝐀𝐒𝐈𝐒

𝐋𝐀𝐑𝐔𝐑𝐀𝐑 𝐓𝐒𝐀𝐑𝐆𝐈𝐘𝐀 – 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐅𝐈𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈 𝐃𝐀 𝐉𝐈𝐍𝐈 [𝐁𝐈𝐋𝐇𝐀𝐙𝐈𝐀𝐒𝐈𝐒]~●●○♦️○●●~~~~
Akwai tarin cutukan dake haddasa fitsari da jini ko fitsarin jini kama daga cuttukan k’oda, shigar kwayoyin cuta mafitsara, cuttukan sanyi da maza ke kwasa jikin Mata, cutar lassa fever, guba cikin abinci dade sauransu.
Toh saide babban abunda kan taimaka a banbance cutar tsargiya wato bilhaziya daga sauran shine sanin labarin yadda abun ya somo da kuma wasu hanyoyin mu’amala na yau da kullum, da kuma inda me larurar ke rayuwa musamman yankunan karkara inda akafi karancin ruwan sha.
Ciwon nada sunaye da yawa domin wasu yankunan kan kira wannan ciwo da tsargiya, wasu suce Katayama, wasu a turance ace snail fever, schistosomiasis, bilhaziasis dadai sauransu.
Ciwo ne da kwayar cutar farasayit (parasites) ke haddasa sa. Wato nau’in halittun dake iya huda fata kamar yadda sauro ke haddasa zazzabin maleriya. Shine ciwo na biyu mafi hatsari bayan maleriya a nau’in cuttukan da parasite ke haddasawa dake shafar milyoyin al’umma tare da kisa batare dama an farga ba.
○○○○○○~□○□~○○○○○○
𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐀𝐊𝐄 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑
Duk wani ruwa da ake iya samun Dodon kodi / ko dodon gori🐌 kamar yadda wasu kan kirasa wato snail toh samun wadancan kwayoyin cuta dake haddasa fitsarin jini ba abune mai wahala ba, Koda kuwa rijiyar cikin gida ce inde da akwaisa, Shyasa ma wasu kan kira cutar da 𝑺𝑵𝑨𝑰𝑳 𝑭𝑬𝑽𝑬𝑹
Amma galibi ana daukar cutar ne asali daga wanka a kududdufi, kogi, ko rafi, domin nan ne zakake ganin kifaye🐟 ana suu, kaguwa🦀 qwaruna da halittun ruwa iri-iri🪱🦑🦐 harma da kananun dodon kodin…🐌🐌 kunga kenan galibi de ana nufin inda ruwa ke taruwa batare da yana tafiya ba, ko kuwa inma me tafiyar ne yana tafiyane de ahanya daya da inma ya tafi zai iya cycling ya dawo ko kuma wani irinsa ya taho daga wani gurin, musamman kuma dama irin wannan ruwan yaran dake wanka ciki har fitsari sukan yi bakasan ma wani yayi ba.
Haka kuma tana faruwa aguraren da ake fita kashi bayan gari wato open defecation, tare da guraren da ake shan ruwa mutane tare da dabbobi, ko kuma ana dibar ruwa kuma ana wanki agurin, ko asami wani yai fitsari acikin ruwan da ake sha, ko kuma ya zamto ruwan saima anshiga cikinsa da kafafu sannan adebo afito wato de guraren da babu ingantaccen ruwan sha, girki, tare da ayyukan yau da kullum.
~~~●●○1○●●~~~
𝐘𝐀𝐃𝐃𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐊𝐄 𝐒𝐇𝐈𝐆𝐀 𝐉𝐈𝐊𝐈𝐍 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐊𝐔𝐖𝐀 𝐒𝐇𝐈𝐍𝐄:
Shi wannan dodon kodin🐌 dake rayuwa a irin wannan ruwan rafi ne ke kasayar da rukunin dattin da ake kira Sakeriye wadda ke rikida ta zama wannan parasite me suna sikistosoma inda daga nan ne dake tana da kaho wato horn ko baki wanda ke bata damar iya huda fatar mutum to shiga, bata bukatar wai sai kana da ciwo sannan ta shigeka… ita da kanta take fasa fata ta shiga, gata da kankantar da ba iya ganinta zakai da ido ba…
Toh a irin wannan yanayi ne bayan dodon kodin ya saketa toh in akai rashin sa’a yara ko manya sun zo wanka kogin, ko sunzo dibar ruwa, ko wanki, ko wasa to shikenan saita makale jikin kafa ko hannun mutum koma duk inda ta samu ya danganta da inda ruwan ya ta6a ajikin mutum… daga nan saita huda fatar ta shiga, tana shiga saita bi hanyar jijiyoyin jini mara iska wato cikin jinin mutum ta VEINS zuwa zuciya ta shiga zuwa kananun jijiyoyin jinin Huhunsa 🫁daga nan daga nan tabi jini mai iska zuwa mafitsara. Toh a wannan halin na tafiyarta acikin jini daga shigarta jiki zuwa kafin ta isa mafitsara take rikida ta zamo Mace da Namijin sikistosomula wanda hakan ke bata damar jawo sindarin furotin na mutum ta lullube kanta dashi wanda hakan kesa sojoji ko garkuwar jikin mu bata iya ganinsu ta yakesu wanda hakan kesa koda sun shiga jika mutum bazaiji wani sauyi na alamun bashi lafiya ba.
A hakane zasu mamayi garkuwar jiki anan cikin jijiyar jini Mace da namijin su barbari juna, wanda barbarar kamar shine yin ciki inda sai iac kuma ta saki kwayakwa cuta (To asannan ne mutum zai fara jin alamun bashi lafiya) wanda akalla asannan kwayar cutar ta shafe kwanaki 14 zuwa 88 acikin jini batare da ansani ba.
Toh asannan ne wannan kwayayen data saki zasu zamto kala iri daban-daban, amma de fitattu cikinsu babu kamar kala uku (3): mansoni, japonicum da kuma hematobiyum:
A cikinsu HEMATOBIYUM sune kwayayen🥚 dake kutsawa ta cikin mafitsara suke bin fitsari suna fita kuma wannan kutsen da sukai shikesa suima mafitsara rauni ake ganin jini tunda dama ajijiyar jinin mafitsarar anan ne asalin mace da namijin sikistoma din suka tsayawa suka barbari juna suka sakesu su kwayayen,
Yayin da Kwayeyen da ake kira MANSONI kuma ke penetrating su kutsa su shiga uwar hanji wanda mutum zai rika kasayar dasu.
Yayin da kwayayen JAPONIKUM jini ke sharosu zuwa wasu sassan jikin irinsu hanta, matsalmama, idanuwa, Saifa, koda, da sauransu suci gaba daba mutum wahala ko illa inba ansami gudummawar magani da zai kashesu ba.
Toh daga nan ne wadancan kwayayen da mutum ke kasayarwa da zubarwa ta hanyar fitsari… idan mai halayyar wankan rafi ne, ko zuwa yai fitsari aruwan da ake sha, ko kashi abayan gari toh duk wanda yasha ruwan nan toh shima ya dauki kwayoyin kenan, haka inma kashine suna nan akasa duk sanda damuna tazo ruwa ya wankosu suka taho wannan kogi ko hanyar ruwa toh duk wanda ya tsoma kafa acikin ruwa ko yasha ruwan toh shima ya daukesu kenan.
Domin bayan ka kasayar ko ka fitsarar dasu aruwa to zasu kuma rikida ne su zama lava ya shiga jikin dodon kodi 🐌 dinnan yasa dodon ya qara sakin wasu CERCARIAE din su zamo sikistosoma… kunga ya zama Life cycle kenan.
~~~●●○2○●●~~~
𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐊𝐀𝐃𝐀𝐈 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐊𝐄 𝐊𝐀𝐌𝐀𝐖𝐀 𝐊𝐄𝐍𝐀𝐍
Eh amutane yafi saide daga cikin wadannan can kwayayen da muke saki suna iya rayuwa ajikin BERA ma, don haka idan ya debo idan har gida da akwai ramukansa toh yana iya kawoma yan gida ciwon ma koda basa shan ruwan rafi.
~~~●●○3○●●~~~
𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐋𝐀𝐑𝐔𝐑𝐀𝐑 𝐒𝐔𝐍𝐄:
Kamar yadda nace inta sikistosoma ta shiga jiki tana yin zirga-zirga ajini kafin taje jijiyar jinin mafitsara inda anan take kyankyasa wanda akalla zata iya shafe kwana 14 zuwa 88, wato sati 2 zuwa 11 matsayin incubation periods nata kafin aji wasu alamu.
Toh kunge kenan bazaka ta6a ji ko ganin alamar komi ba akasa da kwana 13 koda ace da wuri ta gama kyankyasa cikin jikin mutum akalla sai bayan kwana 14 inma ba wata guda ba.
𝐓𝐨𝐡 𝐚𝐦𝐦𝐚 𝐳𝐚𝐫𝐚𝐫 𝐭𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐦𝐚𝐥𝐚 𝐤𝐲𝐚𝐧𝐤𝐲𝐚𝐬𝐚𝐫 𝐭𝐨 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐤𝐰𝐚𝐧𝐚𝐤𝐢 𝐚𝐥𝐚𝐦𝐮𝐧 𝐝𝐚 𝐳𝐚 𝐚𝐟𝐚𝐫𝐚 𝐬𝐮𝐧𝐞:
■- Jin kaikayin jiki
■- Ko ganin kuraje
𝐈𝐝𝐚𝐧 𝐭𝐚 𝐬𝐚𝐦𝐢 𝐤𝐰𝐚𝐧𝐚 30 𝐳𝐮𝐰𝐚 60, 𝐬𝐚𝐢 𝐚𝐟𝐚𝐫𝐚 𝐣𝐢𝐧:
■- Zazza6i
■- Fitsarin da jini
■- Ciwon ciki
■- Tari
■- Kashi da jini walau gudawa ko me tauri
■- Ciwon jiki, musamman tsokokin hannu da kafafuwa
A yayin da duk wadancan kwayaye suka kammala riqa suka fara rarrabuwa masu yin mafitsara nayi, masu zuwa cikin hanji nayi toh sai su soma haddasa rauni gami da tabbai ajika ta cikin ciki bata waje za aga hakan ba toh shine: 𝐬𝐚𝐢 𝐦𝐮𝐭𝐮𝐦 𝐦𝐮𝐬𝐚𝐦𝐦𝐚𝐧 𝐲𝐚𝐫𝐚 𝐚𝐟𝐚𝐫𝐚 𝐠𝐚𝐧𝐢𝐧 𝐚𝐥𝐚𝐦𝐮𝐧:
■- Karancin Jini
■- Rama ajika
■- Yawan kasala
■- Naqasu wajen koyon abubuwa (learning disabilities)
~~~●●○4○●●~~~
𝐌𝐄𝐍𝐄𝐍𝐄 𝐈𝐋𝐋𝐎𝐋𝐈𝐍 𝐖𝐀𝐍𝐍𝐀𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑
Bayan daukar dogon lokaci batare angano cutar ba ko anmaganceta, musamman kamar yadda nace yankunan karkara wasu guraren ma ba asibitoci, wasu kuma asibitocin sha katafin babu kayan aiki, wasu kuma ma’aikatan basa samin bita abune mai sauki sukasa gano ciwon ta alamominsa.
Don haka daga illolin ciwon ana iya fuskantar:
■- Ciwon ciki tare da kumburinsa ta yadda ruwa zai taru aga ciki kamar ankifa kwarya (Ascites)
■- Ciwon hanta tare da kumburinta, aji ciki yai tsir-tsir in an danna
■- Ciwo ko lalacewar hanji, ta yadda kila sai an yanke wani sashinsa
■- Ciwon kirji tare da jin bugawar zuciya far-far da sauri da sauri.
■- Ciwon Huhu da matsalar numfashi
■- Ganin kurji a dubura
■- Ciwon mafitsara, musamman (Bladder Cancer)
■- Wasu lokutan kwayayen kan tafi har kwakwalwa: a irin wannan za’a ga mutum na farfadiya ko jijjiga, ko shanyewar 6arin jiki ko kuma cutar laka ya zamto kafafunsa basa aiki, amma ga sama hannayensa kalau yana iya amfani dasu.
■- Ciwon saifa, itama tana iya kumbura sosai mutum yaita ciwon ciki, ko kuma ya zamto babu ciwo sosai amma in tsautsayi yazo garin wasa aka bugesa aciki ko kuma ya fadi ta gaba toh tana iya fashewa wanda sai an gaggawar zuwa anyanketa.
Wanda in aka yanketa kuma toh nan ma tsugune bata kare ba sai mutum ya lura da kansa sosai domin garkuwar jikinsa ta sami matsala don haka bazata iya yaki da cuttuka sosai kamar da ba. Ya zamo immunocompromised yanzu shima.
~~~●●○5○●●~~~
𝐒𝐔𝐖𝐀 𝐊𝐄 𝐂𝐈𝐊𝐈𝐍 𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑
Yara ko mutane masu wanka a rafuka ko kogi, ko kududdufi sune kan gaba wajen hatsarin kamuwa
Haka inkana rayuwa ko kuwa kana yawan tafiye-tafiye zuwa yankunan da akasan da kwayoyin cutar kuma musamman ya zamto kana zuwa ka shigi ruwan, ko kai amfani wajen wanka da ruwan batare da tsaftacesa ba
Mutane masu sana’ar kamun kifi suma suna cikin hatsarin kamuwa.
Mutane masu zuwa yin wankin tufafi rafi.
Mutanen yankin da ake zuwa bayan gari, ko gefen titi ai fitsari da bahaya (open defecation)
𝐌𝐄 𝐘𝐀 𝐃𝐀𝐂𝐄 𝐀𝐘𝐈 𝐈𝐃𝐀𝐍 𝐌𝐔𝐓𝐔𝐌 𝐍𝐀 𝐓𝐔𝐍𝐀𝐍𝐈𝐍 𝐊𝐈𝐋𝐀 𝐘𝐀𝐍𝐀 𝐃𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍 𝐀𝐉𝐈𝐊𝐀
Hanzarta zuwa aga jam’in lafiya ko likita ai masa bayanin ta yadda ake tunanin kila ankamu da ciwon duk da ba’a fara jin alamun komi ba. Shi kuma daga nan zai binkice ko ya bukaci gwaje-gwajen da suka dace kafin baka magani.
~~~●●○6○●●~~~
𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐀𝐊𝐄 𝐆𝐖𝐀𝐉𝐈𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑
Matakin farko wasu lokutan in alamu sun fara bayyana daga bayanin da za aima likita da tambayoyin dazai abashi amsa tare da zurfin iliminsa yana iya gano ciwon batare da ansa mutum ma ya kashe kudin gwaji ba.
Haka kuma ana iya tura mutum laboratory yayo gwajin kwayoyin cutar acikin jini, ko kuma ta hanyar kar6ar sample na bahayarsa.
Idan anmakaro ana tunanin cutar tayiwa jiki lahani sosai likita na iya sa ai harda hotuna su (ultrasound, CT scan, Abdominal Xray, ko hoton bututun hanji COLONOSCOPY) musamman akwai kumburin ciki…
Haka in mutum ya fara fuskantar ciwon kirji, tari da sauran alamu ana iyayi hoton kirji (CXR), gwajin zuciya (Echo) Ko gwajin kwakwalwa (MRI/CT SCANS).
~~~●●○7○●●~~~
𝐒𝐇𝐈𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐍𝐀𝐃𝐀 𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐈 𝐊𝐔𝐖𝐀
Eh akwai maganin ciwon ingantacce dake kashe kwayoyin cutar. Kuma wani abun mamaki ma wannan maganin sau 1 ko sau biyu tak kurum mutum zaisha ya wadatar, yini 1 kurum, amma kamar yadda kuka sani bana ambatar sunayen magani arubutuna musamman inde ba OTC bane wato maganin da baya bukatar sahalewar likitoci kafin asha, saboda gujewa illolin shan magani daka batare da sanin abunda kaje yazo ba.
Saide shi wannan magani ana auna nauyin mutum ne, sai ai lissafa yawan milgram din da yake bukata… daga nan sai abashi maganin ya raba biyu, inya sha rabinsa nan take can zuwa awa 4 sai yasha ragowar shikenan.
𝐖𝐚𝐭𝐨 𝐝𝐞 𝐦𝐢𝐬𝐚𝐥𝐢𝐧 𝐢𝐧 𝐦𝐮𝐭𝐮𝐦 𝐲𝐚𝐤𝐚𝐢 𝐧𝐚𝐮𝐲𝐢𝐧 50𝐤𝐠 𝐭𝐨𝐡 𝐬𝐡𝐢 𝐤𝐮𝐦𝐚 𝐦𝐚𝐠𝐚𝐧𝐢𝐧 𝐢𝐧 𝐲𝐚𝐧𝐚 𝐛𝐮𝐤𝐚𝐭𝐚𝐫 40𝐦𝐠 𝐩𝐞𝐫 𝐤𝐠, 𝐳𝐚𝐢 𝐤𝐚𝐦𝐚 50𝐱40 = 2000𝐌𝐆
Za’a bashi maganin 2000mg kode yasha sau 1 nan take, ko ace ya raba biyu yasha 1000mg, bayan awa hudu sai yasha ragowar 1000mg
In nauyin mutum kuma baifi 15kg musamman ayara kunga 15×40 = 600mg kenan kacal yake bukata. Don haka nauyi da shekaru sune mahimmai.
Inde mutum yasha shikenan, bai bukatar karin magani saide bayan shekara guda ana oya kuma qara bashi. Amma idan already mutum ya riga ya hadu da illolin ciwon toh wadannan ma sai anbisu daya bayan daya an magance; misali ga wanda ya zamto har hantarsa takai ga kumbura, ko hujewar hanji, ko ciwon ciki, ko de wani abu daban duk wannan daban za’a magancesu.
~~~●●○8○●●~~~
𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐉𝐀𝐌𝐀’𝐀 𝐙𝐀𝐒𝐔 𝐊𝐀𝐑𝐄 𝐊𝐀𝐖𝐔𝐍𝐀𝐍𝐒𝐔 𝐃𝐀𝐆𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
- Kauracewa tare da tsawatarma yara game da wanka arafi, wasa aruwa, ko wanki.
- Rarraba gurin shan ruwa tsakanin dabbobi da mutane.
- Samar da tsaftataccen ruwan sha; ta yadda inma wannan ne kadai hanyar samun ruwa toh arika debosa a tace, asaka aluf aciki ruwan ya kwanta sannan atafasa shi kafin azuba arobar ruwan sha
- Tacewa tare da dumama ruwa awuta koda na minti 3 ya wadatar kafin ai wanka dashi a irin wannan gurare
- Gogewa tare da wanke kafa da kyau bayan hanya ta ratsa da mutum ta inda dole saida ya sauka ya ratsa ta cikin ruwa. Inka da sanitizer kana iya goge kafafunka da ita.
- Tsaftacce swimming pools da sinadarin chlorine ko yaushe akai akai domin wani bakasan irin jikinsa ba.
- Kula da tsaftar bandakunan mu ko yaushe.
- Kauracewa halayyar kashi a bayan gari afili atafi abarsa musamman gabatowar lokutan damuna, da kuma kauracewa yinsa a inda akasan hanyar ruwa ne bama yinsa kusa da ruwan ba. Inta kama dole sai kayi kashin a bayan gari to daure ka haqa rami inkayi ka gama saika rufe, amma rashin yin yafi dacewa.
- Toshe ramukan beraye tare da kamesu ko samusu guba suci su bar gurin.
- Tallafawa irin wadannan yankuna da famfunan borehole domin rage musu radadin rashin ruwa musamman daga gwamnatoci ko masu wadata daga al’umma.
𝐀 𝐊𝐀𝐑𝐒𝐇𝐄
Da an sami me fama da wannan larura a hanzarta kaisa asibiti kada ace za’ai maganin gargajiya abarsa, kunde ji daga bayanina bame ciwon kadai ke cikin hatsari ba in aka barsa kuma baku tsira ba, kuma bai zama dole kusan kun kamu ba kila sai abu ya 6aci aga gari baki daya a lokaci guda ana tururuwa zuwa asibiti ba lafiya abu ya zamo kamar annoba.
Allah ya kara mana lafiya.
☆☆☆☆☆
[𝐈𝐛𝐫𝐚𝐡𝐢𝐦 𝐘. 𝐘𝐮𝐬𝐮𝐟]