LABARAI/NEWS

Na ziyarci shugaba Buhari ne domin in bayyana masa aniya ta na takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a 2023. TINIBU.

Na ziyarci shugaba Buhari ne domin in bayyana masa aniya ta na takarar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a 2023. TINIBU.
___________

A yau Litinin 10/1/2022 tsohon gwamnan Legas, kuma jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu, bayyana aniyar sa na takaran kujerar shugaban kasa Nijeriya a shekarar 2023

Tinubu ya ce yaje fadar Aso Rock ne a yau domin faɗa wa shugaba Muhammadu Buhari aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

Ya bayyana hakan ne jin kadan bayan ganawar sa da shugaban ƙasar Nijeriya Muhammad Buhari.

Tinubu yaye yayin da na bayyana masa aniya ta nayin takara ban ji abun da ba shi na yi tsammanin ji daga gare shi ba, kai tsaye ya ƙarfafa min guiwa kamar yadda dumokuraɗiyya ta ba ni dama,

Duda yake wannan shi ne karon farko da na bayyana aniya ta amma har yanzu ban sanar mutane na ba tukunna sai da na fara jin ta bakin shugaba Buhari wanda shi ne jagoran mu a jamiyyar mu ta APC a halin yanzu. Bayan na bayyana masa kuma ya nuna farin cikin sa to yanzu lokaci yayi da zan zauna da mutane na mu tattauna kan lamuran a siyasance.

Tunibu yace ya shafe tsawon rayuwar sa yana “Tuntuni fatan zama shugaban ƙasa don haka me ya sa damar baza’a yi tsammanin jin hakan daga gare ni ba.

tsarin dimokuraɗiyya, muke kan don haka dole mu tafi a kan haka”, in ji shi.

Yan Nijeriya meye ra’ayin ku kan Yunkurin Ahmad Bola Tinubu na son gadar kujerar shugaban ƙasar Nijeriya a 2023…?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button