
Gomnan babban banki kasa CBN ya fayyace gaskiyar maganar aka masu cewa sabon kudin da bankin ya saki basu da kwaliti da kuma karko
A wata tattaunawa da gomnan babban banki yayi da kafar Muryar Amurka VOA ya fayyace ko mai dake tattare da sabon kudi da al fanun dake cikin chanza kudin
Ba iya ka chanza kala kudin akayi ba,gomnan babban bankin kasa CBN emefele ya bayyana cewa kudin da dauke da wata sabuwar tawada kalar ta ta farko a kasa Nigeria
Chanzin kudin dai na cigaba da kawo matsaloli a fadin kasar nan bayan da wa’adin da babban bankin kasa ya bayar da talatin da daya ga wata Janairu
Tun bayan karatowa lokacin al umma fadin kasar nan ke fama da matsaloli musamman yadda suke matukar shan wahala wajen saka tsohon kudin nasu a bankuna don chanza musu zuwa sabo
Duk da cewa majalisar ƙasa tare da ta jihohi sun mika kudirin su na ganin cewa gomnan babban bankin kasa ya kara wa’adin daina karbar kudin ,sai dai babu tabbas din cewa za’a kara wa’adin ya koma nan da wata shida kamar yadda yan majalisa suka butaka