Islamic ChemistLatest Hausa Novels

Tsamiyar Biri na Magance Manyan Cututtuka 6

Tsamiyar Biri na Magance Manyan Cututtuka 6

magunguna 6 da tsamiyar biri ke yi ma mutum

Masu iya magana kan ce “Da magani a gonar yaro” ko kuma suce “Ga wani a kan matar sarki, da da ido, da ta gani.” Wannan shine kwatankwacin muhimmancin da wasu ababen da muke amfani dasu suke dasu a wajenmu, musamman wajen inganta lafiya, amma bamu sani ba.

bincike masana wanda ya zayyano muhimmancin cin ‘Tsamiyar biri’ gad an Adam, shi dai tsamiyar biri wani nau’in itace ne mai tsami, yana rufe da busashshen bawo baki mai gashi gashi a jikinsa.

Karanta muhimmancin cin tsamiyar biri ga jikinka anan:

1– Yana maganin miyagun sinadarai a jiki masu haifar da dutar daji (Cancer)

2– Yana maganin cutar hawan jini

3– Yana sanya daidaito a bugawar zuciya da kuma daidaita numfashin mutum

4– Uwa Uba tsamiyar biri na maganin cutar zazzabin cizon sauro (Malaria)

5– Tsamiyar biri riga kafi ne ga cututtukan ido dana zuciya

6– Rankatakaf, tsamiyar biri na kara karfin garkuwar jikin dan Adam.

Kira ga jama’a da daure ana amfani da ire iren yan kananan itacen nan masu saukin samu da saukin kudi saboda muhimmancinsu, ta haka zamu dinga kare kanmu daga cututtuka, kuma dama masu iya magan sun ce “Rigakafi ya fi magani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button