RASHIN SANI YAFI DARE DUHU KAHON DA SARKIN KANO YA BAWA SHUGABAN KASA

RASHIN SANI YAFI DARE DUHU KAHON DA SARKIN KANO YA BAWA SHUGABAN KASA
Mutant da dama sun cika da mamakin wai menene wannan Sarkin Kano ya damkawa Shugaba Muhammadu Buhar Kasancewar Sarkin Kano masanin Al’ada ne, shiyasa yayi masa kyautar Fulani, ta al’ada
A Cikin kahon Riga ce wadda ake kira BULLAM KO FARIN KANO riga ta masu mulki, Riga ce wadda sai kasaitattun Sarakuna ke saka ta
Riga ce wadda ba’a saka ta sai ranar Fita Kunya
A jerin Rigunan Hausa wannan Riga ta cikin kaho tana daga Riguna mafi girman Daraja Don haka ne Mai martaba ya yiwa Shugaba Muhammadu Buhari kyautarta a matsayinsa na mutum mafi kololuwar daraja a kasa baki daya
Wanda wannan daddiyar Al’ada ce tun bayan zuwan Fulani kasar Hausa madallah da Samun Sarki masanin Al’ada, mai kuma Farfaɗo da al’ada