Islamic Chemist

MAGANIN MATSALAR FITSARI

MAGANIN MATSALAR FITSARI

MAGANIN MATSALAR FITSARI_*

TAMBAYA:

Assalamu Alaykum Mallam Allah ya saka ma da alheri duniya da lahira, kuma Allah ya jikan mahaifa ameen.

 

Mallam Don girman Allah ka taimaka min da Addu’a ko magani, wallahi mallam inaje yin fitsari, yana daukan lokaci kamin ya fito kuma kadan kadan yake fitowa kuma bladder na yana ciwo, mallam wallahi haka kawai ya fara min ciwo. Fitsari yana fitowa kadan kadan kuma in ya fito yana yankewa.

 

:

*AMSA*

:

 

Wa’alaikumussalam warahmatullah.

 

Dangane da wadannan matsalolin naka, zata yiwu matsalar acikin bladder dinka ne. Kuma zata yiwu ko Prostate cancer ne yake haddasa maka wannan.

.

Ya kamata kaje babban asibiti su dubaka, watakil zasu gane ainihin abinda yake damunka, kuma zasu baka maganin da ya dace dakai.

.

_Amma kafin nan ga wasu abubuwa kaje ka jarraba. Insha Allahu za’a dace:_

_(1). Ka samu ‘Ya’yan Kabewa Cokali 7, ‘Ya’yan Kankana ma cokali 7._

_Ka nika kowanne daban daban._

_(2). Ka samu tafasasshen ruwa, ka zuba garin ‘ya’yan kabewar nan Cokali guda aciki._

_(3). Ka barshi ya huce (ba wai sanyi ba) sannan ka zuba Zuma aciki, sai kasha da safe kafin karyawarka da minti 15._

_(4). Da yamma kuma sai kayi ma ‘ya’yan Kankanar nan haka. Sannan kasha. Kuma zaka maimaita haka har sati guda._

.

_*(2)* Ka samo Katuwar Albasa guda 1. Ka yanka gida 4 sannan ka dafata da ruwa kofi guda._

_Idan ta dahu, ka tace ruwan, Sannan ka zuba Zuma sosai acikinta sannan kasha._

_Insha Allahu wannan zai maka maganin Basur mai kaikayi, ko mai tsiro, ko basur mai Jini, ko ciwon Cancer, ko Ciwon mafitsara, ko Ciwon Qoda, ko tsakuwar Qoda.

 

“`Allah ta’ala yasa mudace“`

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button