LABARAI/NEWSFadakarwaIslamic Chemist

Gyaran Fuska da Kurkum

Gyaran Fuska da Kurkum

Gyaran Fuska da Kurkum

 

 

Ki samu kurkum sai ki daka, daga nan sai ki hada da dakakkiyar alkama, sannan ki hada da man zaitun.

 

Daga nan sai ki shafa a fuskarki ko a jikinki. Bayan awa biyu ko uku sai ki wanke fuskarki ko jikinki da ruwa mai dumi.

 

Hakan yana cire kwayoyin cutar da ke makale a kofofin fata.

 

Yadda Za Ki Yi Amfani Da Kurkum Wajen Gyara Fatarki Kurkum na dauke da sinadarai da dama kamar su, bitamin B6 da bitamin C da sauransu. Kuma yana rike fata yadda ba za a sami rauni .

 

Yawan amfani da hadin kurkum na sanya fata musamman ta fuska laushi da santsi da kuma haske. Don haka, ya kamata kada a manta da wannan kurkum idan an zo kwalliya. ta zama sakakkiya ba.

 

Amfani da kurkum na sanya sabuwar fata fitowa da wuri a inda tsohuwar tAmina

 

•A sami garin kurkum da zuma cokali daya da ruwan lemon tsami kwatan kofi. A kwaba su sosai har sai sun yi laushi.

 

Sannan a shafa a fatar fuska a bari ya jima na mintuna 15 sannan a wanke da ruwan dumi. Yin wannan hadin na hana kurajen fuska fesowa.

 

Za a iya yin wannan hadin kamar sau daya ko biyu a sati domin samin ingantaccen sakamako.

 

•Amfani da kurkum na rage gautsin fuska. A kwaba kurkum da nono ko kindirmo. Sannan a wanke fuska kafin a shafa hadin a fuska. A jira na tsawon mintuna 10-15 kafin a wanke. Za a iya jarraba wannan hadin a kullum bayan an yi wanka.

 

•Idan ke mai yawan aiki a karkashin rana ce, ya kamata ki samu kurkum kadan da kindirmo mai yawa sai ki rika shafa wa a inda kunan rana ta bata fuska. kunan rana na sanya fuska ta zama kamar mai shafe-shafe don haka wannan hadin zai magance wadannan matsalolin.

 

•Ko kun san cewa kurkum na magance bakar fatar karkashin hammata? To! A sami zuma kamar cokali daya sai a hada da ruwan lemon tsami kamar cokula 3-4 sai a zuba garin kurkum kadan sannan a kwaba a shafa a karkashin hammata a bari ya jima na tsakwon mintuna 10-15 kamin a wanke

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button