Latest Hausa Novels

ABU UKU MASU SAUKI DA MATAN AURE KESO MAZAJEN SU RINKA YI MUSU

ABU UKU MASU SAUKI DA MATAN AURE KESO MAZAJEN SU RINKA YI MUSU

Gwargwadon halayyar magidanci zuwa ga iyalinsa ko matarsa gwargwadon imaninsa kenan… karka dad’a karka rage. Duk wanda kaga ya fiye kuntatawa tare da hantarar matarsa da nuna ko in kula baka yi laifi ba in ka kirashi da mara imani domin bashi da imanin kam.

Akwai abubuwa da musulunci ya nema ga duk maigida domin jin dadin kansa ba wani ba. Wadannan abubuwa ukun basu da tsada kuma ba’a kashe ko kobo ciki. Amma in kana yinsu suna gyara matsala lalatacciya sama da dubu sai dae abun takaicin cikin magidanta 1000 da wuya ka samu 3 masu yi gaba daya sauran sai uban korafi akan matsalar da sune sanadinta.

GA SU JAMAR HAKA

■ NA DAYA

Idan mace ta tsantsara kwalliya, ko tayi adoo, ko ta gyara gida ta sharesa tas, ko kuma tayi abinci koh ta shirya yara fes suka tafi makaranta…..

 

Abinda kurum ake so kuma takeso kace shine kaai amma Allah shi miki ALBARKA.. Samun mace irinki zai yi wahala…. chaabb wai wai wai ….. da ban aureki ba da nayi asara da angama dani….

 

Irin wannan tsantsareriyar KWALLIYA,, irin wannan TSAFTA,, irin wannan Abinci ina ci kunnena na Rawa….. in banda kishi da kaza da kaza ai da sai in bude wajen abinci ki rika yiwa mutane muna tara dukiya domin duk wanda yaci sai ya dawo.

 

Kaga in kana haka wallahi dadin da zata ji aranta tare da girman sakon daka isar cikin wadannan kalmomin gareta ba kadan bane suna da tarin yawa.

 

Amma ku fadamun mutum nawa ne a yau zai ci abinci ya kira matarsa yace abincin nan yayi dadi Allah ya saka miki da Alkhairi ??

Amma ranar da Gishiri bai ji ba, ranar da aka makara da yan mintuna kadan abinci bai sauka ba in ya shigo kamar zai tashi Alkiyama. Ni ban yadda ba, ni za a kewa haka, ba’a gama.da wuri ba, waye waye…… Wannan toh babbar matsalace ba halin mutumin kwarai bane komai dukiyarka kuwa.

■ NA BIYU

Idan ka mata ba daidai ba kace wance yaki… na gane ban miki daidai ba… Allah ya baki hakuri

Allah ya baki hakuri… kaga de kalmomin duka basu wuce sekons 3 na agogo ba ka fada ka gama. Allah ya baki hakuri nayi kuskure. Ko kuma kace kiyi hakuri zan gyara…

Sakon dake shiga zuciyar mace in taji wannan ba karami bane wlh.

Amma sai kaxo kayi Abu kuma ka kama wani cin magani ko da magana tayi sai ka hayayyako mata kamar zaka dake ta.

Alaji wannan ko ba matarka ba ba halin mutanen kirki bane Sam wlh.

■ NA UKU

Idan ta shiga damuwa…. toh ka fita damuwa. Misali tana yanka ma salad ko tana yiwa yara wani abu sai ta yanke da wuka…. sai kai maza ka taso da gudu da ka rike wukar kana fadin eeyyyyah subahanallahi  Ina ma nine na yanke…. Inalillahi sannu… yaya za’ai? Ba wani abu de…? Ko asibiti zamu tafi.

Duk ka nuna ka rude ka damu, kace mutafi asibiti … sai tace Aa’h maigida barshi ai abun ba wani me girma bane. Sai kace ai abinne nake ga kamar sai anje asibiti…. sannu kinji.

Ko kuwa a kai ta asibiti ba lafiya amma ta farka taga kai ta fara gani a tsaye ko zaune kusa da ita. Ka tsaya kana duba agogo⌚ yaya kin farka? Me kikeso? Me zaki ci akawo miki?……. subahanallah ai malam kagama cinyeta da yaki.

Itafa mace bafa duniya ce ta dameta ba, Ba ruwanta da mulkinka, da kudinka, da iliminka, da karatunka, da matsayinka, ita duk wannan baya d’ad’ata da kasa. Abunda take so kurum ka damu da ita.

Saboda dadin kalma manzon Allah (SAW) yasan sunan AISHA Harafi biyar ne amma inyazo sai ya gajarceshi ya cire harafin karshe. Yace yaa; “A’ysh”, “A’ish” “e’sh” “Ash” ko “Ay’sha…… Sallallahu Alaihi was’salam duk yana fadar hakan.

Toh in kana haka kana gyara sunan sai taji dadi. Amma kurum malam ace kaida matarka ambatar sunanta kake kuru-kuru ai abun babu tsari ko kadan.

Amma don Allah ina kalubalantarku cikinku duk mazajen nan dake cewa mata basu da kirki, mata kaza da kaza, mata suna son duniya….. Don Allah don ya rasulillahi mutum nawa ne ke wadannan abubuwa ukun acikin ku???? Wlh kunsan bakwayi.

Duk wanda yake abubuwa 3 din can kaga mace na ta masa yawo da hankali toh wallahi kace ya saketa ba abokiyar zama bace karma ya 6ata lokacinsa.

Don haka ga sakon fiyayyen halitta nan idan mun bi mun kiyaye zamuji dadin rayuwar aure komi irin lalacewar da ake ganin kamar auren yayi.

Sai karin wani abu da zai taimaka muku shine;

♡-ku ilmantar da matan in kunga suna da rauni,

♡-Ku dau nauyin kula da lafiyarsu

♡-Ku biya musu hakkinsu na saduwa kada ku zaluncesu

♡-Ka rika mutunta ta ka mutunta iyayenta da yan uwanta kamar yadda take mutunta naka.

Allah kasa mu gyara. Ka azurta mu da ingantacciyar rayuwa agidajen aure amin.

ustaz usman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button