LABARAI/NEWS

A BABI NA TSARKI TARE DA SALLAH

A BABI NA TSARKI TARE DA SALLAH
🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍

Malam ke cewa; Idan mutum sai bayan yayi sallah ne sai ya tuna cewa jikin tufafinsa akwai najasa, walau ta [fitsari, kashi, maziyyi, ko Jini] ko kuwa a ďuwawunsa ya mance yayi kashi bai wanke ba, ko kuwa yai fitsari batare da yai tsarki ba kuma gashi yaje har yai sallah.

Toh abunda mutum zai shine;
Sai yaje ya kama wajen da najasar take ya wanke, ko kuwa ya canza wani tufafin sannan ya canza sallah.

Haka idan kashi ne duwawunsa da katsewa kurum yai bai wanke ba koh kuwa fitsari ne yai bai tsarki ba nan ma sai yaje ya wanke ko yai tsarki ya canza sallah. AMMA idan ya zamto lokacin sallar wato mukutarinta har ya wuce…… Toh sallarsa tayi ba sai ya canza ba.

Eh bazai canza ba! Misali: Ace mutum yai sallar Azahar ko La’asar da najasa ajikinsa ko tufafinsa amma bai tashi tunawa ba sai lokacin sallar Magariba… sannan ne ya tuna cewa kai ai sallah kaza ko sallar la’asar da nayi bani da tsarki ko kuwa da najasa kaza ajikina…. Toh wannan sallar basai ya saketa ba, sallarsa tayi tunda har lokacinta ya fita a sanda ya tuna, amma da ace lokacin bai fita ba toh sai ya canza wata.


TOH IDAN KUMA ALWALA MUTUM YA MANTA FA

Ma’ana ace sallah ce mutum yayi amma sam baida alwala, sai daga baya ya tuna bayan lokacin wata sallar already har ya shiga, ko kuwa ma bai jima da idarwa ba nan ta ke ya tuna ai sallar dana idar yanzu kam banma yi alwala ba ashe… Toh HUKUNCIN anan Baka da sallah, kurum dama kamar ma bakayi sallar bane, domin Babu sallah ga wanda bashi da alwala.

Don haka sallah batare da alwala ba koda lokacinta ya fita saika rama, amma iya wannan sallar guda da kayi batare da alwala ko taimama ba kadai din zaka rama.

Baza ace tunda azahar ce kayi babu alwala ba har sallolin la’asar, magariba ko isha din da kayi suma sun rushe ba tunda ajere suke…. A’ah iya wacce kai babu alwala ita kadai zaka rama insha Allahu.


TOH IDAN KUMA SALLAH DA JANABA CE FA

Wato misali; mutum yai sallah amma ashe da janaba ajikinsa ya manta, bai tashi tunawa ba sai bayan wani lokaci ko bayan wasu kwanaki ko shekaru… Toh hukuncin ana shima kamar na me mancewa da alwala ne.

Muddin ka tuna to dole koda anshekara talatin ne ka tuna cewa sallah kaza da kai lokaci kaza lallai kana da janaba ajika tohfa saika ramata. Sannan anan ma iya wannan sallar kadai da kayi cikin janaba zaka rama, sauran sallolin da suka biyo bayan wannan duk suna nan insha Allahu.


TOH IDAN KUMA LIMANCI NAYI DA JANABA ALOKACIN FA ??

Wato ace mutum shine liman kuma ya zamto sanda ya jagoranci sallar yana da janaba ajika ya manta, Toh anan hukuncin shine duk sauran Mamu wato wanda suka bika sallar su sallarsu tayi, baruwansu, kaine kadai zaka canza sallah,

Kuma koda ace kana sallamewa assalamu alaikum ne saika tuna cewa kana da janaba toh bazaka cewa kowa komi ba, wato bazaka ce kai kui hakuri ku canza sallah ba bani da tsarki… A’ah kai kadai ta shafa, banda su, su sallarsu tayi insha Allahu, kaine zakaje kai wanka ka dawo ka canza sallah.


IDAN KUMA SALLAR NA BARI DA GANGAN FA LOKACIN BANAYI

Wato idan shaidananci yasa mutum yabar sallah da gangan na wasu lokuta abaya wanda amma ayanzu ya shiryu ya dawo yana yinta ko yaushe… Toh hukuncin shine; muddin ka balaga sanda ka barta tohfa saika ramata.

Duk da jawabin malami ya kasu biyu anan; Wasu sunce basai mutum ya rama ba; yayin da wasu sunce dole sai mutum ya rama.

Toh nima anan na tafi akan dole mutum sai ya rama! Saboda me?

Domin idan ka kuskura ka dauki wancan hukuncin na cewa basai ka rama ba saboda ai kamar alokacin kai kafurci ne na addini wato kabar musulunci, tunda munji daga annabi (SAW) cewa duk wanda yabar sallah da gangan tohfa ya kafurta, yabar musulunci….

Toh idan har ko ka yadda cewa; ka kafurtan, kabar musulunci ne a lokacin; Tohfa komi naka na baya dakai ya rushe:
■ Idan ka ta6a sallah kafin ka dena a wancan lokacin tohfa sallar ta rushe,
■ Idan ka ta6a hajji hajinka ta rushe,
■ Idan kana da aure aurenka ya lalace,
■ Idan ka ta6a azumi tohfa azuminka ya rushe…
■ Komi de na musulunci daka ta6ayi kafin ka shiga barin sallah tohfa ya rushe muddin ka yadda ka tafi akan cewa basai ka rama sallar ba daka bari abaya din ba.

Toh kunga wannan hukuncin ai yafi tsauri, amma wanda bai san haka ba ko ba’a bude masa karatun ba ai zaiga shi yafi sauki da kwadayi kurum.


■ Toh amma idan kuwa ya zamto ka yadda cewa Eh gara ka rama din; Toh hukuncin anan iya wadancan sallolin daka bari bakai ba kadai zaka ramo, baza ace tin wancan lokacin har zuwa yau ba duk sallolinka basu ba. A’ah

Hakanan wajen ramuwar zaka jerosu ne kamar yadda kabarsu suka subuce ma ne… Wato Azahar, La’asar, Magriba, Isha’, Asuba Haka zakaita jerosu.

■- Sannan a shawarar malamai sunce kada ka rika biyan bashin sallah ta wuce ta kwana 5 arana. Wato kaga salloli 5 sau 5 kaga na kwana biyar kenan rana, toh sun wadatar.

Saboda idan ka wuce na kwana biyar ana tsoron zaka iya ka rika yinta ba’a natse ba. Ita ko sallah paki-paki ba sallah bace, wasa da addini ce.

Hakazalik koda ace bazaka iya tuna ta tsawon shekara nawa ce ta kuccema ba zakaita ramuwa ne ba adadi har sai randa kai da kanka kaji cewa kai, sallolin nan zuwa yanzu ya isa ace na ramasu. Toh inde kaji ka gamsu da cewa ka ramasu toh shikenan.


Sai kuma ai kokari aga ba’a kuma sake da sallah ba, domin farkon abunda za’a fara dubawa a gobe kiyama shine sallah, inta wuce komi zai zo da sauki, inkuwa bata cika ba tohfa duk abunda aka dauko saide al’amari ya qara rincabewa.

Malamai muna rokonku da inkunga kuskure de toh ariqa nusar damu ana gyara mana, ko yaushe shirye nake na kar6i gyara.

Allah baya kar6ar aiki bisa jahilci, dole saida ilimi da sanin hukuncinsa don haka mu daure mu nemi ilimi bayin Allah.

Allah ka taimakemu tsaida sallah tare da yinta akan lokaci amin.

✍🏼
[Ibrahim Y. YUSUF]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button