Daga Malaman muLABARAI/NEWS

A DAURE A KARANTA PLEASE 

A DAURE A KARANTA PLEASE 

A DAURE A KARANTA PLEASE

 

Watarana wani Gaye neman auren wata baiwar Allah a wani gari. Duk lokacin da yaje hira takan kawo mishi ruwan sha a jug.

 

Rannan da yaje hira sai kakar ta tace: “yau ga kunu mai daɗi na damawa angonah maza ki kaimar kice inji Amaryar shi ce ya sha”.

 

Haka kuwa akayi tazo ta tambayeshi tace: “yau kaka tamaka kunu mai daɗi wai idan zaka sha”.

 

Gayen yayi murmushi yace mai zai hana ni sha?

 

Sai ta koma cikin gida ta ɗauko wa gayen kunun, da tazo daf da zata tsuguna ta ajiye kunun a kusa dashi saita zame ta fadi ƙasa jug din kunun ya suɓuce a hannunta inda kunun ya zuba a jikin gayen ya ɓata mishi wata sabuwar galilar shi mai tsadar gaske.

 

Hankalin budurwar ya yi matuƙar tashi akan ta ɓata mishi kayan shi. Budurwarnan tama rasa meye zata cemar. Shi kuma gayen tsabar ɗokin yadda yake sonta ko ajikinshi hankalin shi yana kanta ne yana cewa da ita: “sannu my dear, inadai bakiji ciwoba sannu ko, yanata kokarin dagata da rarrashin ta”.

 

Da ya tayar da ita taga yadda kunun ya ɓatamar kayanshi taje ta debo ruwa tana zubamar tana bashi hakuri yana wankewa ita kuma hankalin ta a tashe.

 

Gayen yaga yadda ta ɗaga hankalin ta cikin murmushi sai yace mata: “haba sweetheart! Meye hakane kam so kikeyi ki ɓatamin rai? Don kunu ya zube a jikina shine kike wani kuka, gaskiya ki daina kada raina ya ɓaci”. A haka abun yawuce kamar ba’a yiba.

 

Bayan wani ɗan lokaci sai Allah Ya yi aurensu, inda har suka samu karuwan yara.

 

Watarana maigidan yadawo daga kasuwa zai ci abinci. Baiwar Allah taje ta kawo mishi abinci ta ajiye, saita ta koma dauko mishi ruwan sha. Da ta dauko mishi ruwan shan daman ya tuɓe garen shi ya ajiye a kan kujera, sai cikin kuskure garen ya harde kafar matar ta faɗi kasa har goshin ta yafashe ruwan data riƙo a jug ya zube a jikin maigidan nata.

 

Nan take maigidan ya miƙe ya murtuƙe fuska yana muzurai kamar wani kafiri, kamar wanda acid ta zuba mashi a jiki. Ya nata bambami bai damu da taji ciwon ba yana: “ke dai wallahi bansan ranar da zakiyi hankali ba, kwata-kwata baki da nitsuwa a rayuwarki, idan banda wawta da rashin hankali meye zai jawo haka? Ke dai kam Allah Ya yi wadaranki wallahi jaka kawai”.

 

Karshe dai ɗan wannan abunda yafaru sai da maigidannan ya saki matar tashi akan ta zuba mishi ruwa sanadiyyar hardewa da tayi ta faɗi kasa…. 😢 😢 😢

 

Yan’uwa masu hankali, mu dubi yadda wannan al’amari ya faru da idon basira, Mu yi nazarin wannan abin da idon basira, lokacin da yake nemanta da aure, kunu ne mai zafi ma tazubamar a jikin sabbin kayanshi kuma a layi bama a gida ba ammana koya damu harma nuna wa ya keyi ae bakomai, ta daina damuwa. Amman sai gashi bayan sunyi aure, ordinary ruwa wanda bamai zafi ba ya zama kamar ruwan dalma ko acid. Mu dubi wancan lokacin inda damuwar shi ina dai ba taji ciwo ba, amman yanzu ga goshinta na jini koya damu dajin ciwon nata shi dai kawai ta zuba mishi ruwa a kayan shi tamar laifi.

 

Yan’uwa maza masu hankali, ya kamata mu gyara, ya zamto soyayyar bawai a layi aka baro ta ba, a kaita gida shi yafi dacewa.

 

Allah Yasa masu irin wannan halin su gane su gyara su tuna cewa umurni ne Allah Ta’ala Yayi na a kyautatawa mata inda Yake cewa: “…. Wa ashiruhunna bil ma’aruf”.

 

Allah Ya mana jagora Ya bamu ikon Kyautatawa Ameen

 

Abdullahi ✍️

 

.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button