LABARAI/NEWS

a kan soyayya wani matashi ya kashe abokin takararsa a garin girei jihar Adamawa

Akan Soyayya wani matashi ya kashe Abokin takararsa, a garin Girei jihar Adamawa

Wani matashi dan shekaru 38 a duniya mai suna Benedict Haziel ya kashe abokin takararsa, mai suna Luka wanda suke neman budurwa, daya mai suna Blessings a karamar hukumar Girei ta jihar Adamawa

Matashin mai suna Benedict ya kashe abokin karawar nashi ne ta hanyar caka masa wuka a mazaunan sa, inda ya yamu munanan raunuƙa wanda a karshe yayi sanadiyar mutuwar sa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar a hayin gada karamar hukumar Girei da ke Jihar Adamawa. Bayan tsa in tsa ya shiga tsakanin samarin biyu akan budurwar tasu mai suna Blessings wacce kowannesu ke ikirari akan cewa budurwar shi ce.

Tuni dai rundunar yan sanda a jihar Adamawa ta cafƙe wannan wanda ake zargi da kisan kai din wato Benedict

Sai dai wanda ake zargin ya bayyanawa hukumar yan sanda akan cewa Blessings buduwar shi ce kuma ya biya kudin sadakin ta har naira dubu 150, amma duk da haka Luka ke bibiyar ta duk da yasha yi mishi gargadi akan ya rabu da ita domin ita din ayanzu kusan matarsa ce tunda yabiya sadakin ta amma Luka yaki ji yana bibiyar Blessing din wanan ne dalilin dayasa shi kuma ya fusata ya afka mishi da makami

Kawo yanzu dai wanda ake zargi da kisan ana cigaba da tsare shi a hannun hukumar
yan sanda

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button