LABARAI/NEWS
A Katsina Mabiya Shi’a Sun gudanar da gwanon Tunawa da haihuwar ƴar Annabi

A Katsina Mabiya Shi’a Sun gudanar da gwanon Tunawa da haihuwar ƴar Annabi
A Birnin garin Katsina an hango Dubannin Mabiya Shi’a maza da mata tafe Suna rera waƙe ga ƴar Annabi wato Nana faɗimatu (AS) bisa tunawà da ranar Haihuwarta
Jerin gwanon ya samu Halarta dubannin mabiya Shi’an daga ɓangarori daban-daban na faɗin Jihar Katsina
Mabiyan sun fito gwanin ban Sha’awa tafiya cikin Sukuni cikin ƙamshi tare da rero baitika masu daɗi ga ƴar Manzon Allah (SAW) wato Nana Faɗimatu (AS) Kamar yadda Suka Saba a duk Shekara
Bugu da ƙari an fara jerin gwanon lafiya an kuma kammala Lafiya Allah ya karawa Annabi Sallallahu alaihi Wasallama daraja