A labarai da muke samu cewa Ma’aikatan Bankuna ma suna karba cin hanci kafun su sa maka kudade ka a account

A labarai da muke samu cewa Ma’aikatan Bankuna ma suna karba cin hanci kafun su sa maka kudade ka a account
Wasu ma’aikatan Bankunan kasuwanci na Nijeriya sun fara karɓar cin hanci kafin su canja wa jama’a sabbin takardun Naira
Wasu ƴan kasuwa a babbar kasuwar sun koka cewa ma’aikatan Bankunan dake kasuwar suna canja kuɗin ne kawai ga duk wanda ya basu cin hanci
ƴan kasuwar sun bayyana adawar su da tsarin ne lokacin da Kwanturola na babban bankin Nijeriya CBN ya shiga kasuwar domin ci gaba da wayar da kan ƴan kasuwa game da muhimmancin canja takardun Nairar akan lokaci
Ya ce halin da ake ciki yanzu ma’aikatan bankunan kasuwanci su mayar da canja takardun Nairar wata kafa ta cin hanci da rashawa
Sun ma ƙayyade nawa mutum zai biya idan kana son canja dubu goma sha biyar misali to Naira dubu ashirin za ka biya a cewar wanda Abun ya ritsa dasu