LABARAI/NEWS

Abba Kyari da yaransa Sun Kashemin Miji tun watan 4 na shekarar data wuce,

Abba Kyari da yaransa Sun Kashemin Miji tun watan 4 na shekarar data wuce, amma sai yau 7/4/2022 nasani bayan hukumar yan sanda daga ofishin Shugaban Yan Sanda sun fara gudanar da bincike bisa umarninsa.~ Cewar Samira Matar Bashir Dahiru Daura.

Ta cigaba da cewa, bayan kama mijin nata a watan 3 2021, ya sanar da ita cewa ga inda yake, kuma sun tura kudaden daya bukaci a tura domin a bada belinsa, amma daga bisani sai ta dena jin duriyarsa, daga karshe dai tayi tattaki har ofishinsu a abatuwa tare da rakiyar wani kwamishina na Yan Sanda, amma sai Mataimakin Abba Kyari mai suna Sunny yace ai an maidashi legas, saboda laifin da ake zarginsa da aikatawa a legas ne ba anan ba, sannan kuma ana zarginsa da fashi da makami.

Tace batada halin zuwa legas neman mijin nata, amma sai tasamu taimakon wani jami’in Yan Sanda daya taimaka mata har Shugaban Yan Sanda na Najeriya yaji kukanta, kuma nan take ya bada umarnin binciken halin da kuma inda Bashir Dahiru yake.

Bayan gayyatar yaran DCP Abba Kyari, sai gaskiya ta fara bayyana cewa ai yayi ciwo ne na maleriya, wanda suka ruga dashi Asibitin Yan Sanda sukaki karbansa saboda ciwon ya tsananta, sannan daga bisani suka wuce dashi Babban Asibitin Koyarwa dake Gwagwalada inda likita ya tabbatar masu da cewa Bashir Dahiru ya mutu.

Bayan asirin mutuwar Bashir Dahiru ya tonu, sai kuka fara kokarin bata masa suna cewa ai Bashir Dan fashi da makami ne, sama da shekara goma, sai dai kash! Bashir Dahiru yana aiki ne tare dasu indama har ya rika saka hotonsa tare dasu yaran DCP Abba Kyari kamar yanda kuke gani a wannan hoton.

Yanzu dai wasu daga cikin wadanda ake zargi suna hannu inda ake cigaba da bincike.
In baku manta ba dai DCP Abba Kyari da mataimakinsa Sunny suna gidan yarin kuje inda ake tuhumarsa da safarar miyagun Kwayoyi bayan dakatar dashi aiki da hukumar yan Sanda tayi bisa zarginsa da Mu’amala da wani Dan damfara da ake kira Hushpopi.

Daga karshe dai Samira tace, sun kwashi kusan miliyan daya a asusun bankinsa inda wanda ya gaya mata ya nemi ta sakaya sunansa, saboda tsoron kar shima su kasheshi.

Zamuci gaba da bibiyan wannan karar in Allah ya amince, kuma zamu rika baku bayanin duk halin da ake ciki. Mun gode

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button