ylliX - Online Advertising Network ABIN DA YA FARU DA SIYAMA ƳAR SHEKARU 3 A DUNIYA - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

ABIN DA YA FARU DA SIYAMA ƳAR SHEKARU 3 A DUNIYA

ABIN DA YA FARU DA SIYAMA ƳAR SHEKARU 3 A DUNIYA

Siyama ta rasu ranar Alhamis 29-09-2022 da misalin ƙarfe 4 na yamma a dalilin fyaɗe, da ake zargin wani mutum mai suna Idi (baba Idi) ya yi mata. Baba Idi ya kai kimanin shekaru 40 ko sama da haka, wanda ke zaune a Lungun Alh Halliru a unguwar Gama da ke ƙaramar Hukumar Nassarawa.

Ya yi mata fyaɗen ne a ranar Talatar da ta gabata. Kimanin kwanaki shida da suka gabata ne baba Idi ya ɗauki Siyama zuwa ɗakinsa, inda ya yi mata wayo ya ba ta alewa, kana daga bisani kuma ya yi lalata da ita, kuma ya tsoratar da ita akan cewa lallai idan ta sake ta sanar da mahaifinta, to sai ya kashe ta da almakashi kuma ya haɗa ta da magen gidansu ta cinye ta.

Siyama ta kwatanta yadda ya ɗora mata almakashi a wuya akan zai yanka ta idan ta faɗa wa Abbanta.

Bayan shigarta gida ne za a yi mata wanka aka lura da jinin da ke fita daga gabanta, inda da aka tambaye ta me ya same ta, sai ta sanar cewa baba Idi ne ya ba ta alewa sannan ya yi mata wani, kuma ya gargaɗe ta akan idan ta sake ta sanar da mahaifinta zai kashe ta. Siyama ta kuma roƙi mahaifiyar tata akan don Allah kar ta sanar da mahaifinta.

An garzaya da Siyama asibiti, inda likitoci suka tabbatar da an sadu da ita ne ta ƙarfi da yaji. Sun kuma ba da shawarar hanyoyin da za a bi don kula da lafiyarta.

Jami’an tsaro sun cika hannu da wanda ake zargi, inda suka kai shi CID ofis don gudanar da bincike. Lokacin da Siyama ta gan shi cikin ankwa, ta razana sosai tana faɗin me ya sa aka faɗa wa Abba? Ya ce zai kashe ni da almakashi kuma zai haɗa ni da magen gidansu”.

Kashe-gari ne da safe Allah Ya yi mata cikawa, iyayenta sun tabbatar har ta mutu tana faɗin ya ce zai kashe ta da almakashi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button