LABARAI/NEWS

ABINDA YA FARU JIYA A KOTU BAYAN LAWYOYIN NDLEA SUN GABATAR DA SHAIDUNSU A GABAN KOTU

ABINDA YA FARU JIYA A KOTU BAYAN LAWYOYIN NDLEA SUN GABATAR DA SHAIDUNSU A GABAN KOTU

Ban Taba Alaka da Abba Kyari ba, Ban taba ganin Abba kyari ba , kuma Abba Kyari Bashi da Alaka da Cocaine da muka kawo Nigeria daga Ethiopia.

Mai Gidanmu ne mai Suna Emeka ya bamu Cocaine akan mu kawo Nigeria bayan ya tura Hotunanan mu da aka dauka lokacin da muke Ethiopia zuwa jami’an NDLEA akan idan mun shigo airport na Nigeria suyi clearing namu mu wuce.

Kuma an sanar wa Jami’an NDLEA kalan kayan jikin mu, kuma dana shigo har na basu 10,000 kudin happy New Year.

Muna zuwa Airport na Nigeria bayan anyi clearing namu Sai Yan Sanda IRT suka kama mu suka kawo mu Abuja.

Na yiwa Jami’an ‘Yan Sandan IRT da suka kama mu Tayin Basu Makudan kudade don Su barni na arce anma sunki, har yakai na fada musu cewa zan bar musu cocaine gabaki daya don su bar na arce anma sunki barina.

Daga baya na basu hakuri da kuma yi musu alkawaruruwa masu mahimmanci anma sunki yarda, daga karshe dai suka mika mu nida dan uwana patrik zuwa jami’an NDLEA tare da cocaine da suka kama mu.

Ni nayi mamaki da naga Abba Kyari a cikin wannan case din saboda ba shida alaka da wannan harkar tamu Daga bakin Shaida wanda aka yankewa Hukunci shekaru biyu bayan sunyi yarjejeniya da hukumar NDLEA akan zai basu dukkan hadin kai kuma wanda shine yayi safarar Cocaine zuwa Nigeria mai suna CHIBUNNA PATRICK UMEIBE

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button