Abu 8 na ban mamaki da gurji ke yi a jikin dan adam:

Abu 8 na ban mamaki da gurji ke yi a jikin dan adam:
Gurji da a galibin lokuta ake sa shi cikin rukunin kayan Salad, shi ma kayan marmari ne da ke da matuΖar muhimmanci ga jikin dan adam.
Yana Ζunshe da sinadarai masu Ζarfi irinsu, Vitamins da antioxidants da ke taimakawa wajen warkewa da kariya daga cututtuka.
Gurji na da Ζarancin sinadarin calories, sannan akwai ruwa sosai a jikinsa da sinadarin fiber, hakan ya sa yake da kyau wajen taimaka wa jiki da ruwa da rage Ζiba.
A wannan maΖala za mu zayyana hanyoyi 8 da cin gurji zai taimaka wa lafiyarku, bayan samun bayanai a tattaunawarmu da wata Ζwararriya a fannin abinci mai gina jiki kuma malamar makaranta a Kano, Maijidda Badamasi Burji.
- Sinadarai masu gina jiki:
Gurji kusan ruwa ne baki dayansa, don kashi 96 cikin 100 na kayan itacen ruwa ne zalla
Gurji ba shi da sinadarin calories sosai mai sanya Ζiba sai dai yana kunshe da vitamins da minerals masu matuΖar muhimmanci.
Kowane guda wanda ba a fere ba, yana kunshe da wadan nan sindaran:
π Calories:
π Carbs:
πProtein:
π Fiber:
π Vitamin C:
π Vitamin K:
π Magnesium:
π Potassium:
π Manganese:
Ba lallai sai an cinye guda za a samu biyan buΖata ko waΙan nan sinadaran ba, ko raba shi aka yi gida uku aka ci kashi Ιaya to za a samu duk waΙan nan sinadarai yadda ake bukata a jikin dan adam.
Sannan gurji kusan ruwa ne baki Ιayansa, domin kashi 96 cikin 100 na kayan itacen ruwa ne zalla.
Idan ana son tabbatar da ganin ya yi aiki yadda ake bukata, to kar a fere shi, ya fi amfani idan aka cinye shi har Ιawonsa.
Yana maganin ciwon damuwa da saisaita lafiyar ΖwaΖwalwa
- Sinadarin Antioxidants:
Yana kunshe da sinadarin antioxidants da ke bayar da kariya daga kamuwa da cutuka irinsu kansa da ciwon zuciya da hanji da garkuwa daga wasu cutukan.
Maijidda ta ce cin gurji zalla na bai wa mutanen da shekarunsu suka ja garkuwar da za ta inganta lafiyarsu na tsawon lokaci.
- Taimakawa jiki ya samu isasshen ruwa:
Ana iya sarafa gurji ta hanyo daban-daban ko yin Ζwadonsa.
Ana iya sarafa gurji ta hanya daban-daban ko yin ΖwaΙonsa.
Akwai mutanen da ke da matsalar shan ruwa, wanda hakan ke jawo illa ga lafiyarsu. Sai dai rungumar dabi’ar cin gurji na iya maye wannan gurbin.
Bincike ya nuna cewa kashi 96 cikin 100 na gurji ruwa ne zalla, kuma wadanda suka raja’a wajen cin sa shi kaΙai ko ba sa shan ruwa za su kasance cikin wadatacciyar lafiya da kariya daga cutuka.
Sannan yana hana jiki bushewa kana yana gyara fata.
- Rage Ζiba ko tumbi:
Cin gurji na taimakawa wajen rage Ζiba ta hanyoyi daban-daban.
Na farko sinadarin calories Ιin da ke ciki babu yawa. Don haka duk cin da za a masa ba ya sa Ζiba.
Don haka ana iya sarrafa shi ta hanyoyi da dama cikin abinci ko lemu ko ruwan sha.
Sannan, yawan ruwan da ke jikinsa na taimakawa wajen rage Ζiba ko tumbi idan ana amfani da shi a kai-a kai.
- Taimakawa wajen yaΖi da ciwon suga:
Bincike da dama sun nuna cewa gurji na iya taimakawa wajen taΖaita ciwon suga da kuma wasu ilollinsa ga jikin dan adam.
Yawan cin gurji na narkar da suga a cikin jini don haka yawaita cinsa na hana kamuwa da ciwon suga ko diabetes.
- Inganta narkewar abinci da ba-haya cikin sauΖi:
Akwai mutanen da ke tsuma gurji na sa’o’i kafin su sha ruwan.
Gurgi na saisaita kitse a cikin jini da hana tsufa ko yamushewar jiki.
Cin gurji na taimakawa ciki da samun bahaya cikin sauki.
Rashin samun bahaya ko wahala da cushewar ciki abu ne da ke addabar galibin mutane a wasu lokutan, don haka yawaita cinsa na kawo sauΖi da waraka saboda yawan ruwan da yake kunshe da shi.
Hakazalika sinadarin fiber da ke cikin gurji na taimakawa wajen narkewar abinci.
- Yana hana kansar hanji da saisaita kitse a cikin jini
Yawan cin gurji na hana kamuwa da ciwon daji ko kansar hanji.
Sannan gurji na saisaita kitse a cikin jini da hana tsufa ko yamushewar jiki.
- Ni’ima ga mata da gyaran fata
Gurji na Ζarawa mace ni’ima idan aka markada shi da madara ko yoghourt.
Hakazalika ana iya shafa shi a fuska ko jiki domin yana maganin Ζonewar fata sakamakon zafin rana.