LABARAI/NEWS

Abubuwan Dake Hana Mata Sha’awar Namiji Idan Suka Soma Girma

Abubuwan Dake Hana Mata Sha’awar Namiji Idan Suka Soma Girma

A wasu lokutan baya, munyi bayanin yadda karamar mace take da sha’awa. Ita kuwa wacce ta manyanta burinta ta samuwa gamsuwa a lokacin jima’i.
Ma’ana, ita mace mai karancin shekaru kuma wacce batasan maza ba kamin aure, bata sanin dadin Jima’i har sai sannu a hankali ta saba.
A lokacin data saba kamin ta soma zuwan Kai, kawai sha’awa ne da ita, duk yadda namiji ya shigeta yana kawowa itama zata ji ta gamsu. Amma daga lokacinda ta kwarai ta soma zuwan kai tasan dadin jima’i babban burinta shine muddin za a fara Jima’i da ita baza ta gaji ba har sai bayan ta gamsu, ma’ana ta kawo. Wanda a baya ba haka bane. Ana shiga ana fita ita duk abu daya ne a wajenta.
Mace tana kara shekaru tana kara jaraba. Har sai ta kai munzalin daina al’ada a wannan lokacin ne sha’awar ta yake raguwa ga wasu matan. Wannan yasa muddin tsoho ya aure mace mai karancin shekaru zai kasa gamsar da ita idan tafiya ya dau hanya. Sai dai abun tambaya anan shine, mai yasa maza sukan haura shekaru sama da 70 amma suke sha’awar Jima’i, ita kuwa mace data haura 60 ga wasu matan basu da sha’awa sam? Wannan shine amsar da zamu amsa akan wannan darasin.

Wani hikima da Allah SWT Ya saka a cikin al’adar mata na duk wata akwai motsawa mace sha’awar ta na jima’i. Daf, lokaci da bayan kammala jinin al’adar mata, lokutane da suke matukar motsa musu sha’awar su na jima’i, musamman matan da suke da aure ko suka taba yin aure. Akwai ma matan da har lokacin al’adar su mazansu na jima’i dasu duk da haramcin hakan saboda yadda basa iya hakura. Wannan yasa da zaran mace ta kai shekarunta na daina jinin al’ada sai taji sha’awar ta na Jima’i yayi kasa. Wannan yana daya daga cikin dalili na farko dake hana mata sha’awa idan sun girma.
Akwai kuma matan da tsufansu yake zuwa musu da matsaloli na rayuwa yadda basu da kwanciyar hankalin da sha’awa ma zai zo musu.
Irin wadannan matan ana iya samun duk kuwa da sauransu amma matsaloli na rayuwa ya dabaibayesu yadda ko tunanin Jima’i ma basa yi bare suji sha’awar sa. Amma shi namiji duk irin halin da yake ciki yana samun wata dama akan mace nan take gabansa zai harba ya nemi yin jima’i.
Sannan akwai matsala da rashin lafiya da mafiyawa yawan mata suke fuskanta da zaran sun tasan ma tsufa. Mata masu irin wadannan laluran magungunan da suke sha ana samun masu kashe musu sha’awar su. Da haka ne sai nan da nan sha’awar tasu ke gushewa da zaran sun soma manyanta. Wannan matsalar ma yakan shafi wasu mazan musamman masu ciwon hawan jini da ciwon shuga da ciwon mafitsara duk suma suna hana wasu mazan sha’awa da zaran sun soma manyanta.

Wadannan sune wasu daga cikin manyan matsalolin dake daukewa wasu matan sha’awar su da zaran sun soma manyanta.
Sai dai matan da suke da sukuni na wadata matane da a duk tsufansu suna cikin sha’awa da bukata na Jima’i. Hakan kuwa yana biyo bayan irin yadda suke kula da lafiyansu jikinsu ne. Da kuma cin abincin dake kara musu ni’ima. Irin wadannan matan sukan kai har sama da shekaru 70 suna al’ada kuma suna iya yin ciki su haihu.
Allah Ya wadatamu da lafiya da arzikin da zamu kula da lafiyar tamu.

Abubuwan Dake Hana Mata Sha’awar Namiji Idan Suka Soma Girma

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button