LABARAI/NEWS

ABUBUWAN DAKE RAGEWA MATA DARAJA A WAJEN MAZAJENSU

ABUBUWAN DAKE RAGEWA MATA DARAJA A WAJEN MAZAJENSU

WASU KANANUN ABUBUWAN DA MATA SUKE DA YAKE RAGE DARAJA DA KIMARSU GA MAZAJENSU

Mata da yawa ko kuma mutane musamman Hausa fulani suna fuskantar wata irin matsala a fanni na zamantakewar aure.
Domin kuwa da dama za muga tsakanin wance da wane anyi Soyaiya Mai ban kaye, wadda zata kai ga duk wuya duk tsanani dayansu baya juyawa Dan uwansa baya.
Ma’ana daya ya guji daya. Wasu ma suna iya batawa da kowa duk yadda suke dashi mutukar yayi yunkurin rabasu da junansu, koda kuwa mahaifi ko mahaifiyane. To amma abun mamaki da anyi auren wata biyu uku zuwa shida angama daukin amarci, sai kuma aga wasu fitintinu suna ta kunno kai, kuma a kasa gane meye dalili kamar ba sune wadanda suke son mutuwa da kuma batawa da dangi wasu harda uwa da uba ma.

To a wani bincike da nazari da hukumar nazari akan rayuwar aure da zamantakewa tayi angano wasu kananun matsaloli dake taka muhimmiyar rawa wajen rusa wannan kyakkyawar soyaiya da suka gudunar Kafin a kai ga auren.
Wanda kowanne daga cikin ma’auratan yake aikatawa. Sai dai kusan mata nasu yafi yawa kasancewar su ake bawa umarni.
Kowane bangare tsakanin mata da maza yana da tashi matsalar amma tunda dai nan aji ne na mata zalla zamu yi magana akan abinda ya shafi matan kawai.
Ga kadan daga cikin abubuwan da manazartan suka yi tsokaci daga ciki :-

1- GAISUWA BAYAN TASHI DAGA BACCI:- wasu da yawa daga cikin matan wannan karni basu iya cewa da mazajensu na aure “Honey ko dear ko baban wane ko baban wance ko kuma dai Kai Tsaye INA KWANA?” yayin da aka wayi gari lpy especially idan ya dawo daga sallar asuba.
Abinda basu sani ba shine wannan girmamawar tana mutukar sawa Miji ya bude sanitarsa da farin ciki ta hanyar yi masa wannan gaisuwar.
Kamar ba kece in yazo hira ko kuma ya kira ki a waya kike masa hakan ba.

2- ADAWO LAFIYA/SANNU DA ZUWA :- Shima wannan wani common abu ne da yake gagarar da yawa daga bakunan wasu matan.
To bari kuji wani sirri da fadawa miji adawo lpy yake dashi ba.
To be continued….
✍️
Ustaz Usman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button