LABARAI/NEWS
ABUN AL-AJABI GIDAN MUTUWA A GARIN TADURGA TA KARAMAR HUKUMAR ZURU DAKE JIHAR KEBBI

ABUN AL-AJABI GIDAN MUTUWA A GARIN TADURGA TA KARAMAR HUKUMAR ZURU DAKE JIHAR KEBBI
Wannan gidan da kuke gani ana kiransa da gidan Mutuwa Yana wani gari da ake kira Tadurga acikin Jihar kebbi
Mutanen garin basu san wanda ya gina gidan ba hakazalika basusan wanda yake rayuwa a cikin gidan ba Sannan idan dare yayi za’aga hasken wutan Nepa ta ko ina acikin gidan duk da cewa babu wata wayar wuta da ta sauka a cikin gidan
Abunda yafi bada tsoro shine babu wata kofa ta shiga cikin gidan balantana Gaje duka gidan yana kewaye ne da katanga
A wasu shekaru wani matashi yayi yunkurin sanin menene yake rayuwa a cikin gidan nan take yayi tsalle ya haura katangar gidan daga lokacin ba’a sake ganinsa ba har yau