LABARAI/NEWS
Abun Al’ajabi wasu mabarata sun ki karbar tsohon kun domin ba’a karba

ABIN AL’AJABI Wasu Mabarata Sun Ƙi Karɓar Sadakar Tsohuwar Naira 1000 A Kaduna
A jiya ne wasu gungun mabarata suka ki amincewa da tsofaffin takardun kudi na Naira 1,000 da wani Basarake ya ba su a babbar hanyar Kano-road dake Kaduna
mabaratan su uku ne suka yi wa wani matashi birki a kan keken guragu a lokacin da ya sauka daga motar safa ya basu kudin amma basu karba ba
A lokacin da ya fahimci suna neman abin hannu sai mutumin ya dauki takardar tsohuwar naira 1000 daga cikin jakarsa ya mika wa babban mabaraci daga cikin su. ukun
Sai dai abin mamaki sunƙi karɓa cewar su yanzu an daina karɓar tsohon kuɗi inda suka bukaci ya basu sabon kudi