Latest Hausa Novels

AHIR DIN KU ZINDIKAI DA MUTANEN BANZA

AHIR DIN KU ZINDIKAI DA MUTANEN BANZA

An samu wasu baragurbin Musulmai musamman zindikai da sauran mutanen banza makiya da’awar Sunnah suna kokarin cin mutuncin Malama Zainab ‘yar marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Kano

Laifin Zainab Ja’afar shine don tana yiwa ‘yan uwanta mata Tafsirin Al-Qur’ani Maigirma, sai wannan ya zama abin suka da cin mutunci a gareta

Duk abinda ya kamata ta rufe a jikinta ta rufe, bata bayyana cikin tsiraci ba, ta bayyana cikin shiga na kamala da mutunci bisa karantarwan addinin mu na Musulunci, kuma uwa uba wa jinsin ta na mata take yiwa Tafsiri ba maza ba

Wannan yanayin yasha banban da yanayin hada taro tsakanin maza da mata wanda muma muna adawa da hakan, amma wannan wa ‘yan uwanta mata ne zalla take yiwa karatu, ba laifi bane

Kuma abin takaici, ga karuwai nan na gaban iyaye da karuwai masu zaman kansu manyan ‘yan iska fasikai suna gudanar da lamarinsu na lalata da iskanci babu sutura a jikinsu har a media, kullun suna cudanya da maza duk wani hotel da ake iskanci sun sani, amma basu zama abin suka a gurin mutanen banza ba sai wannan

Allah Ka kare Malama Zainab daga sharrin mutanen banza

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button