LABARAI/NEWS

Ahmad Musa ya gina Makaranta domin tallafawa Ƴaƴan Talakawa a filato

Ahmad Musa ya gina Makaranta domin tallafawa Ƴaƴan Talakawa a filato.

A ƙoƙarin da ya ke cigaba da yi wajen tallafawa rayuwar al’umma mabuƙara da masu ƙaramin ƙarfi, shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafan Nageriya na ƙungiyar Super Eagle, Captin Ahmed Musa MON, ya gina katafariyar makaranta a garin Bukuru da ke yankin Kudancin Jihar Pilato domin tallafawa ƴaƴan talakawa su samu sauƙin biyan kuɗin makaranta.

An buɗe makarantar makonni uku da su ka wuce. An kuma raɗawa makarantar suna: (M&S International School). M ɗin ta na nufin (Musa), wato mahaifinsa. S ɗin kuma ta na nufin (Sarch), wato mahaifiyarsa.

Captin Ahmad Musa ya raɗawa makarantar wannan suna ne domin a riƙa tunawa da mahaifan nasa ana yi musu addu’a kasancewar su ne silar zuwansa duniya har ya samu albarkar rayuwar da ya ke iya taimakon jama’a.

Kasancewar akwai buƙatar albashi ga malamai da sauran buƙatun kula da makarantar, karatu ba zai zamto kyauta ba, sai dai makarantar za ta zamto rangwame da rahusa ga iyayen yara waɗanda ba su da ƙarfin biyawa ƴaƴansu kuɗin makaranta sosai wanda manufar Captin Ahmad Musa shi ne kowane yaro ya samu damar samun ilimi duk ƙarancin gatansa.

Sannan kuma, wannan makaranta da Captin ɗin ya gina, asalinta ita ce makarantar da ya yi, wadda a yanzu ya saye gun ya gina wannan katafariyar makaranta a domin masu tasowa.

Captin Ahmad Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen gudanar da ayyukan jinƙai da taimakon al’umma mabuƙata maza da mata. A kowane lokaci ba ya gajiya da tallafawa mutane. Ya samar da tsare-tsare da dama na tallafawa mutane akan harkar karatu, gami da ba da tallafin jarin dogaro da kai ga matasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button