Videos
A’isha najamu da mai wushirya suna kokarin cin amanar murja kunya

Zargi tuni dai yayi nisa inda ake ganin jarumar masana’antar kannywood A’isha najamu wacce akafi da A’isha izzar so suna soyayya da mai wushirya
Mai wushirya wanda fitaccen dan Tiktok ne ana ganin kamar sun fara soyayya da najamu la’akari da yadda suke hira da kuma kasancewa da junan su
Wanna dai na zuwa ne bayan kwanaki kadan bayan kama abokiyar hamayyar najamu wato murja kunya wanda kotu ta aike da ita gidan gyaran hali
Hakan dai wasu na kallon kamar cin mutuncin ne ga murja kunya biyo bayan yadda ake gani a baya kamar suna soyayya ne da mai wushirya