Latest Hausa Novels

Alaƙar Hausa da Fulani

Mun aura daga hausawa suma sun aura daga gare mu, yayan mu sun zama Hausa fulani kuma musulunci ya hada mu, to tayaya da rana tsaka kawai wasu hamagawa suzo wai su a dole zasu raba mu.
Tayaya hakan zai yuwu.

Mu fulani muna kaunar ko wacce kabila da take mutumta mu, kuma bama son fitina anman idan aka nufe mu da ita to bama tsoron ta.

Har kullum muna yiwa jami’an tsaron mu fatan nasara akan pata garin cikin kasar mu.

Wallahi fulani ba mutanen banza bane suna da hakuri duk inda kuka ga sun afka to tapa su akayi. Indai za’a cire son zuciya, bafulatani dake zaune a daji ba karatu a ina ya sayo bindiga?
Suwa suka koya musu yadda ake yin harbi da bindiga?

Su waye informers nasu?
Suwa ke kawo musu man fetur? Etc.

Ya kamata mu yi wa junan mu adalci mu fada wa kanmu gaskiya.

anman zalunci ne ayi mana kudin goro, tunda shi ta’addanci bashi da kabila a ko woni kabila ana samun na gari Dana banza.
Sannan ku Sani har karcen numfashin mu
ba zamu tapa yin shuru muna ganin ana ci mana mutunci ba, dole zamu ci gaba da yi muku raddi tare da fahimtar da duniya irin sharri da zaluncin da ake mana.

Ku sa ido ku lura zaku gane cewa lalle akwai munafurci a cikin zukatan mafi yawancin masu zagin fulani, sabida yawanci bada sunan su na yanke suke anfani ba, domin kada a gano su da ajendar su.

Allah mun gode daka yimu musulmai a cikin al’umma ta fulani.
Allah ka bamu ikon dauwama a cikin turba ta salihan bayin ka.

Allah kamar yadda ka dirkake fir’auna da adawa tare da sauran azzalumai ya Allah kayi mana maganin muna fukan cikin kasar mu Nigeria.

Allah dan rahamar ka da buwayar ka kada ka kama mu da laifin wawayen cikin mu.

Allah ka gafarta mana kurakuren mu
Ka daukaka gaskiya da masu yin ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button