Latest Hausa Novels

ALAMOMIN SHIGAR CIKI GA MACE

ALAMOMIN SHIGAR CIKI GA MACE

Shin waΙ—anne alamune Mace zata ji kota gani idan tana Ι—auke da sabon ciki ta yadda zata gane tun kafin taje asibiti a tabbatar.

Hakika ba kowacce Mace ce ta kwan da sanin cewa babban abinda ke kawo 6atan wata (wato rashin ganin al’ada ba) shine samun juna biyu ba. Musamman a sabbin aure ko kuma a mata marasa kamun kai

Bayan juna biyu kuma cuttukan dakesa shigar kwayoyin cuta ciki ko bakin mahaifar mace [uterus] sune kan gaba wajen kawo 6atan wata (Rashin ganin haila), ko rikicewar lissafin wata.

SAURAN ABUBUWAN DAKE KAWO BATAN WATA SUN HADA DA;

  1. Shayarwa
  2. Halin damuwa, kuncin ko fargaba
  3. Rashin lafiya a yan tsakanin
  4. Bayar da gudunmawar jini
  5. Rashin zama guri guda
  6. Rashin samun hutu, kamar a masu wasannin motsajiki ko doguwar tafiyar kasa
  7. Wasu lokuta ma harda shan wasu magunguna barkatai walau na asibiti kona gida.

🌻
ME ZAI TABBATAR DA CIKI NE ?

Ma’ana wadanne alamu mace mai juna biyu zataji ta tabbatar ciki ne? Gasu nan a zayyane:

A watannin farko mace zata yi 6atan wata, bayan yan satuttuka, sai ta fara samun;

β– Tashin zuciya da sassafe har da amai a wasu lokutan, koda kuwa bataci komai ba.

β– Saurin gajiya, kasala, koya tayi wani dan aiki

β– Ko Ganin jiri (dizziness) idan tazo mikewa bayan jimawa azaune.

β– Yawan zub da miyau, tare da jinsa yana yawan taruwa ga kuma kauri….

β– Zazzabi amma bame zafi can ba haka de kurum zatake jin kamar bata da lafiya

β– Sai rashin son kamshin abu, koda turarene awasu. Tare dajin za6in wani abun daban wanda kafin ajima saitaji tabar sha’awar wannan ta fara sha’awar wani daban.

BATUN GWAJIN JUNA BIYUN FA

A wanne lokaci ne ake so aje ayi gwajin juna biyun in ana kokonto likita ?

  • Akan tabbatar ta hanyar auna fitsari ko jini
  • Sannan sai ta scanning din hoton ciki, idan ma cikin ne to ta hanyar hoton za’a tabbatar, sannan a tantance shin acikin mahaifa yake yadda akeso ko wajen mahaifa wato [ectopic pregnancy].

A watannin da ciki ya fara tsufa kuma wato yakai kamar wata uku (3).akan ga alamu kamar haka:

β–  Girman ciki ya fara bayyana

β–  Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari.

β–  Awasu akan samu ciwon baya,

β–  Ciwon kirji wato zafin kahon zuci ko kwarnafi saboda β€˜acid’ din ciki na tasowa saman kirji

β–  Sai kuma afara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki (stretch marks) da budewar hanci a wasu da kuma jin nauyi ko ciwon nonuwa.

β„Ή
Ba dole bane kowace mace ta samu dukkan wadannan alamun, amma fiye da rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamun.

Allah ka sauki dukkan masu ciki lafiya aamin

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button