Daga Malaman mu

Alfanun Da Ma’aurata Zasu Iya Somasu Idan Suna Kwana Shinfida Guda

Alfanun Da Ma'aurata Zasu Iya Somasu Idan Suna Kwana Shinfida Guda

Alfanun Da Ma’aurata Zasu Iya Somasu Idan Suna Kwana Shinfida Guda

Zaka yi mamaki ko idan akace maka akwai ma’auratan da basu kwana a shinfida guda? To kada kayi mamaki akwai su da dama kuwa.

Tunda a wannan darasin ba zamu yi magana bane akan dalilin daya sa basa kwana a shinfida daya ba. Zamu yi magana ne akan alfanun da ma’aurata zasu samu idan suna kwana tare.

1: Kara Dankon Soyayya: Ma’auratan da suke kwana a shinfida guda bincike ya tabbatar da cewa suna samun shakuwa da juna fiye da ma’auratan da basa kwana tare. Domin wannan barci tare da suke yi yana sasu su kaunaci juna ya kasance guda bazai iya barciba ba tare da gudan ba. Wannan zai sa rabuwansu koda na kwana daya ne suyi shi cikin sauki.

2: Yana Karawa Garkuwan Jiki Karfi: Wani binciken da masana suka yi sun gano cewa ma’auratan da suke kwana a shinfida guda da juna suna karawa junansu lafiya ta yadda wannan dummin jikinsu na karawa garkuwan jikinsu karfi yadda zasu kare dukkanin wasu cutan da ke kokarin shigansu.

3: Kara Musu Yarinta: Kwanan ma’aurata a shinfida guda yakan sa a kullum su rika jinsu kamar yara koda kuwa sun manyanta. Hakan nan bincike yace yana rage musu tsufa, ya cire musu kamannin tsufa a jikinsu.

4:Magance Hawan Jini: Masana sunce ma’auratan da suke kwana a shinfida guda basa kamuwa da cutar hawan jini. Binciken yace koda ma’aurata suna da cutar na hawan jini muddin zasu rika kwana tare a shifida guda, tuni zasu magance wannan cutar ba tare da sunga likita ba.

Wadannan sune wasu daga cikin alfanun da kwanciyar ma’aurata a wajen guda yake da alfanu a rayuwarsu.

Sai dai wani abun sani shine ba kowani irin kwanciya bane ma’aurata zasu yi kuma su samu wannan alfanun da muka kawo cikin wannan darasin ba.

A darasi na gaba idan lokaci ya samu zamu kawo irin yadda ake kwanciyar samun alfanun da ma’aurata zasu Yi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button