LABARAI/NEWS

Alhassan Ado Doguwa ya nemi gafarar Dan jaridar da ya yiwa mahangurɓa

Alhassan Ado Doguwa ya nemi gafarar Dan jaridar da ya yiwa mahangurɓa

Biyo bayan zarginsa da mahangurba ga wani Dan jarida, Hon Alhasan Ado Doguwa Dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Tudun wada da Doguwa, ya gurfana a Shalkwatar rudunar shiyya ta daya dimin amsa tambayoyin kan karar da Abdullahi Yakubu ya shigar.

 

 

Sai dai Doguwan ya roki gafarar dan Jaridan wanda ya bayyana shi a matsayin abokinsa tun shekaru 30 da suka gabata.bayan hakurin da Doguwan ya bayar shima Dan jaridar da ya shigar dakarar ya yi koyi da halin Annabawa wato hakuri kan balahirar data wanzu tsakaninsa da Doguwan.

Ya dai shigar da karar ne bisa zargin naushi da doguwan yayi a wani taron manema labarai da ya kira a gidansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button