Videos

Ali Nuhu da hamisu breaker sunyi magana akan hotunan Bikin Ado gwanja da jaruma momee Gombe

Ali Nuhu da hamisu breaker sunyi magana akan hotunan Bikin Ado gwanja da jaruma momee Gombe

Wa’yannan jarumai biyu sunyi wata magana mai harshen damo wacce duk wanda yaki zai tabbatar da cewa lallai wannan aure ya tawo kuma akwai shi wanda kuma Ai kasance nan bada jimawa domin yadda ake ganin kannywood sun Shira tsaf domin fara shagalin bikin wanda zai dauki hankalin jarumai

Ali Nuhu dai ya fara da sawa wannan aure akbarka da kuma fatan Allah ya tabbatar da alkhairi sannan yace Allah yakaimu lokacin wanda jin wannan maganar yada mutane suka kara tabbatar da cewa lallai wannan aure ta tawo kuma babu wata tangarda ko zancen kanzan kurege a cikinsa

Shima mawaki hamisu breaker ya tabbatar da cewa suka farin ciki da wannan aure kuma suna fatan ayi lafiya a gama lafiya sannan suna musu fatan samun zaman lafiya a wannan rayuwa ta aure da zasu shiga kuma suna basu shawarar cewa ayi hakuri da juna

Kafin ado gwanja ya fara shirye shiryen auren jarumar anfi dangantata da mawaki hamisu breaker wamda kusan shekara uku ma anyi tunanin tun alokacin zasuyi aure ashe dai ba haka bane kawai dai yakan sakata acikin wakokine amma babu wata alakar soyayya a tsakaninsu wanda mutane suke zargi

Maganganun wa’yannan jarumai biyu sun kwamtarwa da masu kokwanto hankali domin da dayawa mutane sun dauka wannan maganar duk zance ne babu ita ashe abin yananan daram

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button