Nishadi

ALLAH JIQAN BABBAN_BANGO! SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI
😭😭😭😭

ALLAH JIQAN BABBAN_BANGO! SHEIKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI
😭😭😭😭

Sadda duk Ramadan ya doso,
Sai hawayena su feso,
Don tunanin wanda soso,
Bai kai shi a wanke dattuka ba!
😭❀️😭

Dole mui ta zubar hawaye,
Kan rashin bangon Iyaye,
Wanda birni har da kauye,
Ba Su mance nasa khairuka ba!
😭❀️😭

Rabbana ka jikan madubi,
Shaikhana Gumi me magirbin,
Sassabe barna da aibi,
Masani mara qullata da gaba.
😭❀️😭

Shehu dan Mahmuda gwarzo,
Me yawan hakuri da kwazo,
Wanda tunda ya zo ya gunzo,
Bai San takwara a maluma ba.
😭❀️😭

Ka ji babban me shari’a,
Me tawakkali me qana’a,
In ya ce “e” babu a’a,
Ba a San shi da saba alkawalba.
😭❀️😭

Ka ji me tafsir kwararre,
Me farin hali dirarre,
Wanda ko da kangararre,
Ba zai iya Jan sa sui fada ba.
😭❀️😭

Ka ji me ilmin Hadisi,
Me kwabe duk iltibasi,
Bai da homa ko ta sisi,
Kuma bai zam me takabbura ba.
😭❀️😭

Ka ji Alkali na koli,
Me ado da ruwan dalili,
Malamin da ya zam misali,
A cikin ulama’a ba ba’a ba.
😭❀️😭

Ka ji gwarzo me iyar wa,
Al’uma sakon biyowa,
Ga gwanintar shiryatarwa,
Da basira ba da hantara ba.
😭❀️😭

Ka ji me kishi ga dini,
Ga sanin ilmin zamani,
Tarjamar da ya wa Qurani,
Kafin sa ba ai kamar sa din ba.
😭❀️😭

Ka ji wanda ya jure wautar,
Jahilai da nufin ya “yantar,
Tunda bai da nufin muguntar,
Hana Ilmi ba halinsa ne ba.
😭❀️😭

Ka ji shaihi me kawaici,
Me hade duk izgilanci,
Don ya kai Jama’a ga yanci,
Ba wai Su zamo cikin duhu ba.
😭❀️😭

Duniya dai tai asarar,
Jarumin da ya ke isharar,
Al’uma Su rike basirar,
Islamu da zamaninsu duba.
😭❀️😭

Mun rashin mai nuna turba,
Me cikar kima da haiba,
Wanda gulmar masu giba,
Ba ta sa ya ki nuna gaskiya ba.
😭❀️😭

Mun rashin samfur na koyi,
Malamin da ya zam masoyi,
Me farin hali taqiyyi,
Bai dau duniya abar riko ba.
😭❀️😭

Rabbana ka jikan ubanmu,
Bubakar Gumi malaminmu,
Wanda mun shaida dukan mu,
Bai zabi ya tara duniya ba.
😭❀️😭

Jalla rokona gare ka,
Gafararka da jin-kayinka,
Jaddada Su ga talikinka,
A cikin firdausi jalla rabba.
😭❀️😭

Nan na sa aya na huta,
Kantamawy ne ya yi ta,
Wanda rabbu ya wa katarta,
Ba a San shi da raina maluma ba.
😭❀️😭

πŸ™πŸ™πŸ™πŸ™

Abubakar Alkantamawy Nakowa
08022581902

Ke fatan Allah ya jikan magabatanmu da gafara
πŸ™πŸ™πŸ™

24-4-2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button