Islamic Chemist

ALLAH SARKI LIKITA BAWAN ALLAH

ALLAH SARKI LIKITA BAWAN ALLAH

A ƴan watannin nan biyu da nai offline akalla akwai wasu masu larura mutum uku wanda Allah yai musu rasuwa cikin friend list ɗina suke, sun kasance masu bibiyar rubutu na akoda yaushe 2 Maza, 1 Mace.

Dukkansu da larurorinsu na riskesu:

1 Sickler ne,
1 Ciwon zuciya ne da ita,
1 Ciwon hanta,

Alal hakika dukkansu mutuwarsu ta tsayamun, toh saide kwai guda ɗaya wanda mutuwarsa tafi tsaya mun sosai duba da kokarinsa. Shine wanda yake ɗauke da sickler… Ina jin mutumin jihar jigawa ne.

Magana ta domin Allah ni kaina nasan wannan bawan Allahn yana so ya rayu don ya nunan hakan, yana da burikan da yake son cikawa arayuwarsa ba kaɗan ba, yana kuma yin dukkan kokarin da ya kamata inde nace yi kaza tohfa sai inda kokarinsa ya kare, haka iyayensa sun yi kokari dashi. Saide Allah yasa mutuwa ta zamto hutu garesa.

Iya ni dashi muke magana, ba kuma saninsa nai ba a zahiri… Amma ashe yana fadawa mahaifinsa komi dake faruwa tsakanin mu,

Wallahi mahaifinsa saida takai ya turon sakon gaisuwa ta musamman, saboda shi de yaga iya abinda zai iya mun kenan tare da fatan alkhairi. Ni kuma aɓangarena daman nasan me cece SICKLE CELL DX kokarina dama naga de rayuwarsa ta inganta, tunda akomi dama wahala ita ake gudu, mutuwa wannan dole ce ga kowa.

Bayin Allah!
Ubangiji shike kashewa ke rayawa, likita zai dubaka ya baka magani amma Allah shike warkarwa, ilimin likitancin baki ɗaya Allah shine ya ke badashi ga wanda yaso, shiyasa wani ko ya fara baya yiwuwa masa komi sonsa da abin, karshe saide ya canza fanni kuma kaga yai nasara a inda ya canza ɗin.

Toh haka cikin wancan ilimin de Allah ya horewa likitocin iya ganewa da nazartar wasu cuttukan da yadda suke rage LIFE SPAN, har takai ga in ma mutuwa ta tunkaro mutum daga ilimin mukan iya hasashen zuwa sanda zata iya aukuwa.

Akwai cuttukan da in suka sami Bawa sai hakuri, kai kasan warkewarsu da kamar wuya saide maleji kurum, amma galibi kwai wasu shekaru ƙididdigaggu da mutum inya cin masu tohfa inde ciwon ne da kasani anan suka fi mutuwa. Daga ilimin ka kasan basa wuce shekarun sai yan ƙalilan 2 cikin dubu dakan ɗan gota hakan…

Ba yadda ka iya matsayinka na likita wasu cuttukan ade yanzu bamu san nan gaba ba… Wanda CUTAR SICKLER na daga cikin irin wannan larurorin masu ƙididdigaggun zango na rayuwa.

Kunga zafi irin na rumbun gasa biredi…koshi zai rufawa me sickler asiri a lokacin CRISIS ɗinta inta motsa, su kadai suka san ya suke ji cikin jijiyoyin jininsu, tunda zafi ba abune da zaka iya kwatantasa agane ba sai kai kurum da abin ya shafa.

Kuma ba iya zafin bane kamar ana ɗiɗɗigawa mutum ruwan zafi ko dalma haka suke ji a jijiyiyinsu saboda kartar da murɗaɗɗun kwayoyin jininsu kewa bangon jijiyar, shiyasa zakaga yara wuni kuka saboda su sukasan me suke ji har arika yaro ya fiye fitina. Ba haka bane, ko kai babba saika koka

Sickler da kuke gani koda da kulawa tana da hatsarurruka domin takan iya kaiwa ga:

1- Stroke (fashewa ko toshewar magudanar jini a kwakwalwa) wanda ɓarin jiki ka iya shanyewa,

2- Takan haddasa cancer acikin ƙoda

3- Tana sanya lalacewar saifa da matsalmama yadda saide aciresu kuma in aka cire mutum ba shi ba kuma cin maiko ko abu me kitse domin jiki bazai iya ƙonesu ba
4- Lalacewar hanta,
5- Makanta,
6- Gyambo musamman a kafa wanda ke ƙin jin magani, baya ga
7- Kashe sha’awar ɗa namiji koma tasa gaban ya mutu saboda trauma.


Sannan tana da wata illah da wani lokacin in a Namiji ne haka kurum Gabansa zai rika mikewa ba da sunan sha’awa ko wani abu ba, haka kurum zai mike kuma mutum yayi-yayi amma bazai kwanta ba,
a wasu mikewar tanasa azzakarin ya riƙa musu zafi da zogi su rasa ya zasui, wani ma suma zai don azaba, sai anje asibiti in magani bai ba dole sai likita ya huda kan azzakarin abinda ake kira shunt ya zuqe jinin da ya cusheta…

Wanda daga baya komi na iya faruwa, kuma ba lallai shikenan matsalar ta tafi ba, zata cigaba da dawowa inba Allah ya takaitawa mutum wahala ba.

Shi wannan wanda ya rasun yana daga illarta datai masa na haddasa masa sickle cell leg ulcer, wato gyambon kafa…

Kuma gyambon sickler yana da matukar wari, wasu gudun zama dakai ma zasui ba kowa zai jure ba, kuma haka kurum abin ke faruwa bawai ciwo ne mutum zaiji ba ya zamo hakan… Shine zakaga har naman gurin zaizayewa yake, kuma bai jin magani, mutum sai ya shafe shekara sama da 7 ko 10 yana fama dashi inma bai mutu ba. Saide aita dressings don gujewa shigar kwayoyin cuta

Domin abinda ke assasashi shine: Ita sickler baki daya kwayoyin jinin ne ke canza suffa ta yadda bazasu iya ɗaukar iska a wadace ba cikin jini inka shaqa, sannan bazasu iya tafiya smoothly ba cikin jijiyar jini koda manyan jijiyoyi toh ballantana kuma kananu irinsu capillaries da yanzu yanzu sa yage su doɗe.

Toh lalacewa da toshewar ƙananun magudanan jinin can na ƙafa sakamakon gurbatattun kwayoyin jinin masu lanqwasa suffar lauje da jikin ke samarwa, hakan ke hana iska (oxygenation) ƙarasawa can ƙasa ta shiga cikinsu wanda akwana atashi tunda jini baya tsirgawa hakan ke nuna ba iska ma bata tsirgawa toh kunga ko mutum inba iska a huhu ai mutuwa zai, toh rashin iskar ga wadancan jijiyoyin kesa area din fara mutuwa a hankali har dare daya abin ya bayyana kai tsaye… Kamar kurji saika ga abin ya kwaile toh shikenan hanya ta samu saide abu ya cigaba, kana iya kwanciya lafiya kalau amma ka wayi gari da matsalar a kafarka.

Gashi kamar yadda nace ba irin maganin da ba za’ai ba amma kaga kamar ba’a yi, domin dole sai jini na tsirgawa kafin kowane irin ciwo ya warke toh su zirga zirga jini dama koda haka kurum normal babu kyau jikinsu ballantana ga rauni.

Shiyasa a kokarin maganin gyambon har fatar jikinsu walau ta gadon bayansu, ko cinya ko duwawu ko ƙoƙon kai mukan yanka ai mushe mafo da ita agun gyambon musamman inyai rami da yawa matsayin “Skin Graft” amma galibi karshe graft din haka zai lalace tunda ba excellent blood supply…

Wanda akarshe wannan ne kan zamo mabudin hanyar mutuwar masu sickler din saboda kwayoyin cutar dake bi ta kan gyambon su shiga cikin magudanar jininsu su haddasa wato septicaemia.

Shima wannan bawan Allah din har yankar fatarsa anyi andasa agun ciwon amma Graft din karshe ya lalace.

Haka wasu ga munana suffa da sickler takan sa musu: kaga mutum da zumɓutun baki hakora basa rufuwa, ko ƙaton goshi, canzawar launin ido zuwa ruwan ɗorawa ko yaushe, ko kumburin ciki kamar ankifa ƙoƙo.

┈┉┅━💕🌷💕━┅┉┈

Don haka bayin Allah, kamar yadda nasha yin jan hankali babu wata hanyar da zamu kaucewa mace-mace da illolin cutar sickler sama da hanyar binkice kafin Aure, tare da hakuri a ƙauracewa auren in angano cewa haɗin bai dace da juna ba. Munsan da ciwo agama soyayya ace ba aure amma ya kakeyi in late comer yai ma wuff? Dole kake hakuri, shiyasa mukeson kafin ai nisa a soyayya atambayi status din juna aji.

Kunga kamar yadda kuka san in aka gano Mace ko Namijin da ake shirin aure yana dauke da “Kwayar cutar HIV” kai tsaye za’a hakura da auren saboda gudun wahala toh itama SICKLER hakane ba bambanci.

Ya dace ku gujeta kamar haka, ya kamata ku gane hakama mismatch na genotypes ɗin sickler yake da hatsari. Muddin zaka ji tsoron kanjamau toh ya dace kaji tsoron sickle cell disease haka.

Kar ku bari soyayya ta rufe muku ido, saboda galibi kance bakomi baby zan tsaya miki, amma karshe duba da yadda yaron inyazo zaike cin kudi wasu arana aje asibiti sau 3 ko 4 sai kaga ba kunya ba tsoron Allah mutum ya saki matar ya barta da ɗan ko ƴar tana fama har sai in sun mutu.

Muna ganin abinda ke faruwa ka tambayi Mace kaji ta tabbatar da lallai auren soyayya sukai.

Ba daɗi yara su taso da ɗan uwa amma suga yana wahala, wani bin suma suna wahalar musamman in iyayen girma ya fara hawa kansu, har agirma atasa basusan dadin komi na ɗan uwansu ba saide wahalta masa, karshe kuma ya rasu ya barsu da jimami da kuka, baya da kashe kudadeasu yawa kumga abin kwai zafi.

Don haka yan Mata da Maza ya dace kusan Genotypes dinku tun kuna makarantun secondary bama sai lokacin aure ba, hakama aure koda bazawara ace aje ayi, gwajin nan fa bawani tsadane dashi ba, muna fatan ma gaba kadan ya zamo kyauta kamar na HIV.

Ta hanyar hakane kurum zamu kawo karshen ciwon a Africa dama duniya baki daya musamman Nigeria.

Saboda sickler mune a Africa muke fama, mutanen ASIA ko Turai basu da cases ɗin, kurum saide su karanta a littafi… Inkaga mai sickler cikinsu zakaga baƙar fata ne dama mazaunin can, Mune da mutanen mu basa jin shawara muke wahala, biyewa son zuciya maimakon masalaha kesa ciwon cigaba da yawaita har gashi yana daga cikin zafafan daliliai 10 na yawan mace-mace a Nigeria

Amma da ayau zamu canza halin mu gaba ɗaya, muka rungumi gwaji da hakuri in angano rashin daidaito toh ina tabbatar muku zuwa lokaci ƙanƙani ciwon sickler saide tarihi. Kai tsaye zaizo karshe, ai sai ana haihuwar carrier din ciwon zai cigaba, tunda andena ciwon ma nemansa za ai arasa, shikenan gaba babu me cewa kai genotype screening don zakai aure.

Kusan hakan ne ma ga cuttuka irinsu hanta: kirikiri zaka cewa bakar fata ga abinda ya dace amma bazai dau maganarka da mahimmanci ba sai yaga halaka ko abu yai lalacewar da saide ai masa addu’a sannan zai zo yana na dama.

Fatan mutanen mu za’a waye haka, wannan ba batu na haramci ko kace ai addini kaza-da-kaza ko addini baya tare da son zuciya anan, bai yadda ba tunda ansan abinda zai biyo baya…. Yafi muni kace gara ai auren inyaso in ansami ciki ai gwaji in fetus din me sickle cell ne sai a zubar dashi… Da wannan ɓarnar gara hakuri da auren.

Mace ko Namiji rukunin “AS da AS” Ko “AS da SS” sune ba’a son aure tsakaninsu.

Ya Allah ka jikansa tare da sauran waɗanda suka rasu, Allah kuma ka qaramana lafiya.

✍🏻
Ibrahim Y. Yusuf

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button