ALLURA CIKIN RUWA ME RABO KA DAUKA WATA ZANKADEDIYAR BUDURWA A KANO NA NEMAN MIJIN AURE

ALLURA CIKIN RUWA ME RABO KA DAUKA WATA ZANKADEDIYAR BUDURWA A KANO NA NEMAN MIJIN AURE
ta ce ta yafe kayan lefe, amma ba ta son saurayi kazami Wata Kyakykyawar Budurwa a Kano zaman gidansu ya isheta ta kosa tana son ta shiga daga ciki aure take so Saboda yawancin kawayenta duk sun yi aure har da ‘ya’ya.
Wannan tsaleliyar budurwar mai abin tausayi ta ce Samari da Alhazan birni suna ta zuwa gurinta wai suna kaunarta ammma abin mamaki babu wanda yake zuwa da zimmar yin aure sai dai su ce su je otel su kwana
Budurwar ta ce ita ta san kyawun da Ubangiji ya ba ta ga gayu sune ya sa maza suke ta rububin zuwa gurinta da niyar fasikanci
Budurwar ta zargi kyau ta ce kyau ko wahala ga shi yanzu shekarunta 26 ba ta yi aure ba maza suna bata mata lokaci saboda kyawunta