LABARAI/NEWS

ALLURA ZATA TONO GARMA

ALLURA ZATA TONO GARMA

Babban Akanta Janar na Nigeria Ahmed Idris wanda hukumar EFCC ta kamashi da laifin satar kudin ‘yan Nigeria sama da Naira Biliyan 80..

Labarin da nake ganin yanzu na cewa; a tuhumar da EFCC take masa a inda yake tsare, ya ambaci sunan Uwargijiyarsa Ministar Kudi Hajiya Zainab Shamsuna Ahmed, cewa ita ma ta karkatar da wasu makudan biliyoyin Naira ta hanyar mallakar manyan gidajen alfarma a Abuja, Kaduna, Lagos da Kasar Dubai

An bar bayada kura, Shugaba Muhammadu Buhari ba barawo bane, amma ba shakka da alama manyan barayi kuraye sun mamayeshi, tabbas akwai manyan maciya amana da sukaci amanar shugaba Buhari kuma sukaci amanar ‘yan Nigeria

Wallahi ina fatan a samu canjin Gwamnati, mu samu shugaba jarumi wanda zai yiwa mukarraban shugaba Buhari binciken kwakwaf

Duk wansa yaci amanar ‘yan Nigeria Allah Ya tona masa asiri

Arewa Intelligence
22-5-2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button